
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun haɗaka a Arewa maso Gabas, ƙarƙashin Atisayen HAƊIN KAI, sun samu ƙarin adadi mai yawa cikin ƙanƙanin lokaci na kwamandoji, mayaƙa da masu taimaka wa ‘yan ta’adda da ke miƙa wuya ga rundunar sojoji.
Rahotanni sun bayyana cewa, sama da ‘yan ta’adda guda 150 ne suka miƙa wuya acikin wannan makon, wanda idan aka kwatanta da 50 da aka samu a makon da ya gabata, hakan na wakiltar ƙarin kashi 202.
Kafin Mohammed Goni, jami’in yaɗa labarai na rundunar kuma na riƙo, shi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin. A cewar sanarwar, hakan ya faru ne sakamakon hoɓɓasa da dakarun suka yi wajen faɗaɗa ƙaddamar da atisayen leƙen asiri da matsi akan harkokin ‘yan ta’adda daga ɓangaren sojoji a shiyyar.
Rundunar ta bayyana cewa, ci-gaban ya nuna yadda harkokin ‘yan ta’adda ke fuskantar takura musamman kan harkokin zirga-zirgarsu, raba kayayyaki da kuma gazawar ƙoƙarinsu na riƙe mambobi a maɓoyarsu. Haka kuma, rundunar sojin ta ce ta ƙwato wasu makamai da alburusai daga hannun ‘yan ta’addan da suka ajiye makaman nasu.
Ta ce, wannan nasara ta samu ne a sakamakon atisaye mabambanta na sojoji, dabarun sadarwa da ayyukan haɗin-gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula da nufin karya lagon ayyukan ‘yan ta’adda da kwaɗaitar da mambobinsu kan su ajiye makamansu tare da barin harkar ta’addanci. Sanarwar ta ƙara da cewa, baki ɗaya waɗanda suka miƙa wuyan an shigar da bayanansu a na’ura kamar yadda doka ta hukunta.
Rundunar ta kuma ci alwashin cigaba da ƙaddamar da hare-hare akan harkokin ‘yan ta’adda yayin da take kuma kwaɗaitar da matakin miƙa wuya acikinsu da haddasa koma-baya a ɗaukar sabbin mayaƙa da kuma lalata hanyoyin safarar kayan aikinsu.
Rundunar Sojin a matakin ƙasa, ta yaba wa dakarun bisa jajircewarsu tare da kira a gare su da su cigaba da matsa wa harkokin ta’addanci a sassan Arewa maso Gabas lamba domin tabbatar da bayar da kariya ga ƙauyuka da dukiyoyin al’umma da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a shiyyar.
