Yanzu-yanzu: APC ta musanta janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta janye jaddawalin sunayen ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Felix Morka, ya bayyana rahotannin da ke yaɗa hakan a matsayin jita-jita, inda ya ce dukkan wani hukuncin da aka yanke kan kwamitin, za a ji shi ne daga bakin jam’iyyar a hukumance. Da yake magana da ‘yan jaridar a safiyar yau Talata a Abuja, Morka ya ce APC ba ta janye jaddawalin ba kuma ra rahotannin da ake yaɗawa akan haka ba gaskiya ba ne don haka jama’a su ƙaurace musu.

“Jita-jita ba labari ba ne. Idan mutane suna ɗaukar jita-jita, wannan ba labari ba ne. Akwai labarin bogi, sannan akwai labari na gaskiya,” inji Morka. A cewarsa, jam’iyyar za ta fitar da jawabi a hukumance muddin aka samu buƙatar yi wa jaddawalin wata kwaskwarima.

Hakan na zuwa ne bayan yaɗuwar wasu rahotanni a ranar Litinin da ke cewa wai jam’iyyar ta janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓenta domin yin nazari a kai, yayin da aka koka kan waɗansu sunaye acikinsa.

A ranar Asabar ne dai APC ta fitar da jaddawalin yaƙin neman zaɓen nata, wanda aka naɗa Shugaba Tinubu a matsayin shugaba da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin maitaimaki. Haka kuma, an naɗa Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin mataimakin shugaba na biyu yayin da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari kuma aka ba shi muƙamin darakta-janar na kwamitin.

Saidai, an samu cece-kuce acikin fagen siyasa game da sanya sunayen wasu jami’an gwamnati da waɗanda ma sun fuskanci zarge-zargen rashawa yayin da suke riƙe da madafun iko. Amma, sakataren jam’iyyar ya ce APC za ta fitar da dukkan wani sauyi ta hanyoyin da suka dace a madadin barin jita-jita ta yi tasiri acikin al’umma.

By Babaji

Leave a Reply