
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar 24 ga Oktoba, 2026 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fara yawon neman zaɓensa na shugaban ƙasa domin babban zaɓen 2027 da ke tafe a Jihar Kaduna.
Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar na jam’iyyar APC, Abdulaziz Yari ne ya bayyana haka a ranar Juma’a jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja Yayin hira da wakilan fadar.
Ya ce, Shugaban ƙasa ya amince da jaddawalin yaƙin neman zaɓen da suka gabatar masa, inda ya ƙara da cewa daga nan zai zarce zuwa Maiduguri, Jihar Borno bayan gangamin Kaduna.
A cewarsa, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa (PCC) na APC a hukumance, wanda ya kafa ‘yan watanni kaɗan da suka gabata a ranar 14 ga Oktoba a babban ɗakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.
Yari, wanda tsohon gwamna na kuma sanata mai ci daga Zamfara ta Tsakiya, ya ce za a fitar da jaddawalin yaƙin neman zaɓen ga al’umma bayan ƙaddamar da kwamitin.
Ya kuma yi hasashen cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zaɓen Shugaban ƙasa da gagarumar nasara ga Shugaba Tinubu, yana mai dogaro da shurar shugaban da yawan jihohin da APC take mulki.
