NUJ a Katsina ta taya Hannatu Mohammed murna

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ), Reshen Jihar Katsina, ta taya Hannatu Mohammed murna kan zaɓenta a matsayin mataimakiyar shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ), Arewa maso Yamma

Hajiya Hannatu ma’aikaciya ce a gidan talabijin na ƙasa (NTA), Katsina.

A wata takarda ƙungiyar wanda shugaba da sakatare suka sanya wa hannu ƙungiyar ta bayyana cewa zaɓen nata ya nuna ƙwarewarta a jagoranci, jajircewarta a aikin jarida da kuma gudunmuwarta wajen ɗaukaka mata a fannin yaɗa labarai.

Ta ce tana da ƙwarin gwiwar cewa gogewarta za ta ƙarfafa NAWOJ tare da kare muradun mata ‘yan jarida a faɗin shiyyar.

Ƙungiyar ta yi mata fatan alheri da nasara a kan wannan sabon muƙami, tana mai tabbatar mata da goyon bayanta da haɗin kai a kowane lokaci.

By ukarofi

Leave a Reply