Makasa sun yi wa wata mata kisan gilla a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu wata mata mai suna Hafsat da aka fi sani da Mama Mimi a mace a gidan aurenta da ke Unguwar Rimin Zakara a Jihar Kano a ranar Asabar, bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun mata kisan gilla. Rahotanni sun ce, an gano gawarta ne bayan maƙotanta sun koka kan halin da take sakamakon ɗaukar tsawon lokaci ba su ji ɗuriyarta ba, bayan an ce ta fita siyo kayan miya da nufin girki amma ba ta dawo ba.

Wani shaida ya faɗa wa jaridar DAILY POST cewa an yi ta gwada kiran layin wayarta amma babu amsa, inda aka gano gangar jikinta bayan an yi ta ƙwanƙwasa ƙofar gidanta. Ɗaya daga cikin shaidun, wani ya ce an fara zargin wani abu da misalin ƙarfe 3 na yamma a lokacin da Hafsat, wadda ta bar gida domin siyo kayan miya, ba a gan ta ba a waje. Sannan an yi ta gwada kiran wayarta amma ba ta shiga.

Bayan tuntuɓa da jira a wajen gidan, maƙota sun gano cewa an ja ƙofar ne ba tare da rufe ta baki ɗaya ba, inda suka yi yunƙurin shiga ciki. Yayin da aka shiga cikin gidan ne kwatsam sai aka ga Hafsat cikin jini ba ta iya motsi.

Wata shaida mai suna Mumsy, ta faɗa wa jaridar cewa wasu mazauna da fari sun je gidanta suna neman Hafsat bayan sun ɗauka ba ta gida. Ta ce, da fari an ɗauka marigayiyar barci take yi sakamakon an san ta da barci mai nauyi. Bayan mintina 30 ba tare da samun wani labari ba sai ta garzaya gidan domin gano abin da ke faruwa da ita, inda ta ga taron jama’a.

Ganin cewa ‘yan unguwar na fargabar shiga gidan, sai Mumsy ta hanzarta kiran ‘yan uwan Hafsat, domin su zama na farko wajen shiga gidan. Wannan al’amari ya jefa iyalan marigayiyar cikin jimami, inda makusantanta suke kira da a tabbatar da gaskiya da adalci wajen kamawa da gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu a kisan domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply