Ƙarancin fitowar masu zaɓe ya mamaye gwada tantancewar INEC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar da gwajin tantance masu zaɓe (Mock Accreditation) a faɗin Jihar Katsina domin tantance shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027, sai dai gwajin ya samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a yawancin rumfunan zaɓe da aka ziyarta.

Gwajin, wanda aka gudanar a lokaci guda a dukkan mazaɓu 361 na jihar, an shirya shi ne domin gwada aikin na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), fasahar tura sakamakon zaɓe ta hanyar intanet, kayan aiki da kuma aikin ma’aikatan wucin gadi (ad hoc staff) gabanin babban zaɓe.

Ma’aikatan wucin gadi na INEC sun isa rumfunan zaɓen da aka tura su tun da ƙarfe 7:30 na safe domin shirya kayan aiki, yayin da aka fara tantancewa da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

A rumfar zaɓe 07009, Nadada, Daki 9, ƙarƙashin mazabar Wakilin Kudu II a Katsina ta Tsakiya, kaɗan daga cikin masu zaɓe ne kawai suka fito domin tantancewa, lamarin da ya sa jami’an zaɓe suka yi ta jiran masu zaɓe.

Haka ma a rumfar zaɓe 008, Bayan Tashar Kofar Marusa, Layin Zana, ƙarƙashin mazabar Wakilin Gabas II, mazauna yankin sun danganta ƙarancin fitowa da rashin isasshen wayar da kan jama’a da ƙarancin sanin cewa ana gudanar da gwajin.

Sauran rumfunan zaɓe, ciki har da Unguwar Madawaki da Mannar Gangare, suma sun samu ƙarancin halarta. Wasu ma’aikatan wucin gadi na INEC sun ba da shawarar cewa rashin sha’awar jama’a ga zaɓe, rashin ƙarfafa gwiwa da damuwa kan sahihancin zaɓukan da za su zo na iya zama dalilan ƙarancin fitowar.

Da yake sa ido kan gwajin, jami’in hulɗa da jama’a na INEC a Jihar Katsina, Aliyu Adosa Garba, ya bayyana gamsuwarsa da yadda gwajin ya gudana, yana mai bayyana shi a matsayin mai sauƙi kuma mai tsari, duk da ƙarancin halarta.

Ya bayyana cewa an zaɓi rumfunan zaɓe guda biyu a kowace mazaba daga cikin mazabu 361 na jihar domin tantance shirye-shiryen aiki na hukumar gabanin babban zaɓen 2027.

A cewarsa, gwajin tantancewar an shirya shi ne domin tantance ingancin na’urorin BVAS, tsarin tura sakamako ta intanet, tura kayan aiki da aikin ma’aikatan zaɓe a cikin yanayin da aka kwaikwayi ranar zaɓe.

Tun da farko, kwamishinan zaɓe na Jihar Katsina (REC), Farfesa Yahaya Makarfi Ibrahim, ya bayyana gwajin a matsayin mai matuƙar muhimmanci wajen gano gibin aiki da ƙarfafa shirye-shiryen hukumar gabanin babban zaɓe na 16 ga Janairu.

Ya ce gwajin zai bai wa hukumar damar gano raunin da ka iya kasancewa da kuma ɗaukar matakan gyara kafin ranar zaɓe.

“Mun yi shirye-shiryen kayan aiki, mun gwada kayan aikinmu, kuma muna tantance aikin ma’aikatanmu na wucin gadi da kuma aikin na’urorin BVAS da takardun sakamako,”Inji Farfesa Makarfi

“Zuwa yanzu ba mu fuskanci wata babbar matsala ba, amma a ƙarshen gwajin za mu yi cikakken nazari domin gano da magance duk wata matsala da ka iya tasowa,” in ji REC.

Duk da ƙarancin halarta da aka samu a wurare da dama, jami’an INEC sun ce gwajin ya ba da damar tantance muhimman hanyoyin da ake bi a ranar zaɓe, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply