Daga AISHA ASAS
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya samu gagarumar nasara a shari’ar da ta shafe shekaru tana jawo masa matsin lamba na siyasa, bayan wata babbar kotu ta soke rahoton da a baya ya buɗe ƙofar yiwuwar tsige shi daga shugabancin ƙasar.
Kotun Western Cape High Court ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, inda ta bayyana cewa rahoton wani kwamitin majalisar dokokin ƙasar na shekarar 2022 ya saba wa doka, tare da soke sakamakon binciken da kwamitin ya gudanar.
Batun ya samo asali ne daga satar kuɗaɗen da aka yi a gonar shakatawa ta Ramaphosa mai suna Phala Phala a shekarar 2020, inda ɓarayi suka sace dala 580,000 da aka ɓoye a cikin wata kujera mai matashi.
Lamarin ya haifar da zarge-zarge kan shugaban, musamman game da yadda aka gudanar da binciken satar kuɗin da kuma dalilin da ya sa ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda yadda ya kamata ba.
Kwamitin majalisar dokokin da ya gudanar da bincike a lokacin ya bayyana cewa akwai dalilan da ke buƙatar Ramaphosa ya amsa wasu tambayoyi kan lamarin, har ma ya nuna yiwuwar aikata ba daidai ba ta fuskar kundin tsarin mulkin ƙasar.
Sai dai a hukuncin da ta yanke yanzu, kotun ta ce kwamitin ya wuce iyakar ikon da doka ta ba shi, ya kuma yi amfani da tambayoyin da ba su dace ba wajen gudanar da bincikensa.
Alƙaliyar kotun, Nolwazi Mabindla-Boƙwana, ta bayyana cewa kwamitin ya yi manyan kura-kurai na shari’a wajen fahimtar aikinsa.
Wannan hukunci ya kawar da wani babban ƙalubale da ke barazana ga shugabancin Ramaphosa, duk da cewa har yanzu batun na iya ci gaba da kasancewa cikin muhawarar siyasar Afirka ta Kudu.
Lamarin ya kuma sake jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin doka wajen gudanar da binciken da zai iya shafar makomar shugaban ƙasa da kuma cibiyoyin mulki.
