Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar Matasa Musulmi ’Yan Agaji ta ƙasa, Fityanul Islam of Nigeria, ta gudanar da taronta na ƙasa da ƙasa karo na biyu a Kano, mai taken “Samar da shugabanci nagari a Nijeriya ta hanyar tsarin dimokuraɗiyya”.
A taron, manyan malamai da masana sun gabatar da takardu daban-daban kan hanyoyin samar da shugabanci nagari a dimokuraɗiyya.
Tun da farko, a jawabinsa, Babban Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Fityanul Islam na ƙasa, Ustaz Sani ibn Salihu, ya ce manufar taron ita ce wayar da kan jama’a game da zaɓen wanda ya cancanta, ba wanda ya bayar da kuɗi ba.
Ya ce idan mutum ya zo da kuɗi domin a zaɓe shi, amma aka ga bai dace ba, ya kamata ’yan Nijeriya su ƙyale shi da duk wani abu da zai bayar domin a zaɓe shi. A cewarsa, idan aka yi haka za a samu shugabanci nagari, domin duk wanda ya kashe kuɗi domin a zaɓe shi, ana iya cewa riba yake nema.
Ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na biyu da ƙungiyar ke gudanar da irin wannan taro. An fara shi ne a shekarar 2022, inda aka yi taron mai taken zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, domin suna zaune wuri guda.
Ya ce a wannan karon an zaɓi batun shugabanci nagari ne saboda ana gab da gudanar da babban zaɓen 2027.
Taron ya samu halartar malamai, ciki har da Sheikh Muhammad Arabi Abul Fatahi, wanda ya yi bayani kan tarihin rashin adalci da shugabannin Nijeriya suka yi, da yadda aka bar ƙasar a baya ta fuskar ci gaba. Ya ce al’umma ce ya rage wa ta nemi mafita domin samar da shugabanni nagari da za su yi adalci.
Haka kuma, Sheikh Haliru Abdullahi Maraya daga Kaduna ya gabatar da takarda kan yadda malamai za su bayar da gudummawa wajen zaɓen shugabanni nagari da za su yi wa mutane adalci.
Dakta Atika Bala Maiyafe ta gabatar da takarda kan gudummawar mata a siyasa da yadda ake takaita musu damar shiga muƙaman gwamnati, ta hanyar ba su kashi biyu kacal na wasu muƙamai.
Sauran waɗanda suka gabatar da jawabai sun haɗa da Barista Sani Yau, babban lauya kuma mai ba ƙungiyar shawara, da wasu masana.
