APC ta nesanta kanta da wata wasiƙar bogi da ta nemi INEC ta tabbatar da nasarar Tinubu a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta nesanta kanta da wata wasiƙa da ake zargin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya rubuta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), inda aka ce ya buƙaci hukumar ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa jam’iyyar mai mulki, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta bayyana wasiƙar da ta yaɗu a kafafen sada zumunta a matsayin ta bogi, mai cike da ƙeta, kuma wani yunƙuri ne na ɓata sunan shugabanninta da kuma raunana cibiyoyin dimokuraɗiyya.

Wasiƙar da ake zargin an rubuta ranar 22 ga Nuwamba, 2026, kuma aka aika wa Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ta nemi haɗin kan hukumar gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Takardar, wadda ba ta ɗauke da sa hannun kowa ba, ta yi ikirarin cewa shugabancin APC na sa ran INEC za ta yi amfani da hanyoyin gudanarwa da tsarin aikinta wajen tabbatar da ayyana Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sai dai APC ta musanta wannan wasiƙa, tana mai cewa ba Yilwatda ne ya rubuta ta ba, kuma ba ta fito daga ofishinsa ba. Ta kuma jaddada cewa takardar ba ta dace da tsarin sadarwa da jam’iyyar ta tanada ba.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban APC na ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana wasiƙar a matsayin takardar yaudara da aka ƙirƙira domin zubar da mutuncin shugaban jam’iyyar, APC da kuma tsarin dimokuraɗiyya.

Sanarwar ta ce: “Jam’iyyar All Progressiɓes Congress ta yi Allah-wadai da wata wasiƙa da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wadda ake zargin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya rubuta wa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, mai taken ‘Shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu’.

“Wasiƙar da ba ta ɗauke da sa hannu ba, wadda aka sanya wa ranar 22 ga Nuwamba, 2026, ta ƙunshi wani ikirari na ƙarya da ba shi da tushe cewa shugabancin APC na sa ran INEC za ta yi amfani da hanyoyinta na hukumomi, tsarin gudanarwa da ƙarfin aikinta wajen tabbatar da ayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

“Jam’iyyar ta bayyana karara cewa wasiƙar ba ta fito daga Farfesa Yilwatda ba, bai rubuta ta ba, kuma ba ta da wata alaƙa da shi ko ofishinsa. Takardar bogi ce da aka ƙirƙira da mugun nufi domin zubar da mutuncin shugaban jam’iyyar, APC da kuma tsarin dimokuraɗiyya.”

Jam’iyyar ta ƙara da cewa rashin sa hannu ko wata alamar tabbatar da sahihancin wasiƙar ya nuna cewa takardar ta bogi ce, tana mai zargin cewa an yaɗa ta ne da gangan domin yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Haka kuma, APC ta soki wasiƙar bisa karya ƙa’idojin sadarwar jam’iyyar, tana mai cewa ba zai yiwu a fitar da wasiƙa mai muhimmancin irin wannan ba ta wata hanya da ba ta cikin hanyoyin sadarwa na hukuma ba.

Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci wasu mutanen da ba a san ko su waye ba, waɗanda ta bayyana a matsayin masu haddasa fitina a siyasa da yaɗa bayanan ƙarya, su ɓata sunan shugabancinta ta hanyar ƙirƙirar takardun bogi ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “APC ba za ta bari wasu mutane da ba a san ko su waye ba, masu haddasa fitina a siyasa da yaɗa bayanan ƙarya, su jawo wa shugabancinta zubar da mutunci ta hanyar yaɗa takardun bogi ba.

“Mun yi Allah-wadai da wanda ya ƙirƙiri wannan wasiƙa ta wulaƙanci, kuma muna ƙalubalantar waɗanda ke da hannu a ciki da su fito fili, su amsa alhakin abin da suka aikata tare da gabatar da sahihan hujjoji kan ikirarinsu, maimakon ɓuya a bayan rashin bayyana sunansu suna yaɗa ƙarya da haifar da rashin yarda ga cibiyoyin dimokuraɗiyya.

“Domin kauce wa duk wani shakku, APC na nan daram kan ƙudurinta na tabbatar da zaɓe cikin zaman lafiya, gaskiya, ’yanci da adalci a babban zaɓen 2027. Jam’iyyarmu ta yi imani da muhimmancin ƙuri’a, ’yancin INEC da kuma haƙƙin ’yan Nijeriya na zaɓen shugabanninsu cikin ’yanci, ba tare da tsoratarwa, magudi ko katsalandan ba.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kansa ya sha nuna ƙudurinsa na bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya. A wajen tarukan yaƙin neman zaɓe da sauran ganawa da jama’a a sassa daban-daban na ƙasar, Shugaban ƙasar ya sha kira ga ’yan Nijeriya, musamman waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a, da su mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC) tare da sauke nauyin da ke kansu na ɗan ƙasa.

“Wannan wata alama ce karara da ke nuna amincewarsa da tsarin dimokuraɗiyya da kuma imaninsa cewa halaccin nasarar zaɓe ya kamata ya fito daga muradin jama’a da suka bayyana ta hanyar ƙuri’a cikin ’yanci.”

A ƙarshe, shugaban APC na ƙasa ya buƙaci ’yan Nijeriya da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da wasiƙar, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na nan kan ƙudurinta na kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya, gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya da mutunta hukumomin zaɓe.

Jam’iyyar ta ce za ta tunkari babban zaɓen 2027 cikin ƙwarin gwiwa da ladabi, tana mai jaddada cewa duk wata nasarar zaɓe dole ne ta kasance wadda aka samu ta hanyar goyon baya da sahalewar al’ummar Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply