Daga ABUBAKAR A. BOLARI Gombe
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen 2027 na jam’iyyar PDP, Ahmed Shuaibu Gara-Gombe, ya ce babu wata barazana ko tsoratarwa da za ta hana shi shigowa Jihar Gombe, yana mai jaddada cewa ba zai bari a tauye masa haƙƙinsa na ziyartar jiharsa ta asali ba.
Gara-Gombe ya bayyana hakan ne bayan ya shigar da ƙara ga Sufeto Janar na ’yan sanda (IGP), kan zargin sa ido da wasu mutanen da yake zargin jami’an tsaro ne ke yi a gidajen iyalinsa guda biyu da ke Gombe.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, ya ce an sha ganin wasu mutane sanye da fararen kaya suna kai komo a kusa da gidajen, ciki har da gidan da mahaifiyarsa ke zaune da kuma wani gidan da sauran iyalinsa ke zama.
Ya ce wannan lamari ya haifar masa da damuwa matuƙa, musamman dangane da tsaron mahaifiyarsa da sauran ’yan uwansa, tare da nuna fargaba kan abin da ka iya biyo baya.
Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Azubuike Nathaniel, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Gara-Gombe ya miƙa ƙorafi a hukumance ga IGP, tare da sanar da hukumomin tsaro da abin ya shafa a Jihar Gombe, domin gudanar da bincike kan zargin.
Ya ce yana kuma ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa an binciki lamarin tare da ɗaukar matakan da suka wajaba wajen kare iyalinsa.
Haka kuma, ya bayyana cewa tuni aka sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP na 2027 kan lamarin, inda kwamitocin shari’a da tsaro na jam’iyyar ke nazari tare da duba matakin da ya kamata a ɗauka.
Gara-Gombe ya kuma ce yana la’akari da ƙarfafa matakan tsaron kansa idan yanayin ya buƙaci hakan.
Sai dai ya jaddada cewa ba zai amince da shawarwarin wasu da ke neman ya guji zuwa Gombe saboda fargabar tsaro ba.
“Babu wanda zai hana ni zuwa Gombe. Zan zo. Wasu mutane sun shawarce ni da kada in zo, amma babu wanda zai hana ni ziyartar jihata,” in ji shi.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan zargin, gano waɗanda ke da hannu idan aka tabbatar da aikata ba daidai ba, sannan su ɗauki matakin da ya dace bisa doka.
Ya kuma buƙaci hukumomin su tabbatar da tsaron iyalinsa tare da hana duk wani abu da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron al’ummar jihar.
Gara-Gombe ya ƙare da jaddada cewa lamarin ba zai hana shi gudanar da ayyukansa na siyasa ba, ko kuma sauke nauyin da ke kansa a matsayin daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP na 2027.
Ya ce zai ci gaba da amfani da haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki da shiga harkokin siyasar Gombe ba tare da fargaba ko matsin lamba ba.
