Daga JOHN D. WADA a Lafia
An yi kira na musamman ga Kiristoci a Najeriya kada su yi watsi da halayen Kiristanci komai tsananin cin hanci da rashawa da ƙalubalen da al’umma ke fuskanta a ƙasar nan a yanzu.
An yi wannan kiran ne a ranar Lahadi daga babban Fasto na cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) Tudun-Kauri a Lafia Jihar Nasarawa.
Yayin da yake gabatar da wa’azi mai ƙarfi mai taken “Kada ka yi watsi da halayenka na kiristanci ko da a cikin al’umma mai cike da cin hanci da rashawa,” Fasto Makpa ya gaya wa jama’a cewa halin da ƙasa ke ciki a yanzu bai kamata ya zama dalilin da muminai za su sassauta bangaskiyarsu ba.
Yace Kiristoci da dama suna rasa natsuwa a hankali saboda wahala, cin hanci da rashawa, tsanantawa da kuma lalacewar ɗabi’a a cikin al’umma amma ya tunatar da su cewa Allah yana sa ran ’ya’yansa su fita daban su kuma haskaka kamar haske ko da a cikin duhu ne.
A cewar malamin duk ƙasa ko wurin da mumini ya tsinci kansa, dole ne ya riƙe Allah maɗaukaki kuma ya yi koyi da rayuwar Almasihu.
Ya bayyana cewa wannan ne dalilin da ya sa Manzo Bitrus ya ƙarfafa muminai a zamaninsa waɗanda suka tsinci kansu a ƙasashen waje kuma suke fama da matsalar rashin natsuwa.
“Manzo Bitrus ya san cewa muminai za su fuskanci jarrabawa a ƙasa mai nisa. Ya ƙarfafa su kada su rasa asalin su a cikin Almasihu. Wannan ne saƙon da muke da shi a yau. Najeriya na iya zama da wahala, amma kada mu rasa halayenmu na Kiristanci,” in ji shi.
Fasto Makpa ya kuma koka cewa Najeriya tana cikin wuta a yau saboda cin hanci da rashawa ya cinye kowane fanni tun daga iyalai zuwa ofis da kasuwanni da makarantu har ma da wuraren ibada.
Sai dai ya nace cewa Kiristoci dole ne su kasance da Allah koda yake za su fuskanci ƙalubale da jarrabawa da tsanantawa.
“Cin hanci da rashawa yana ko’ina. Amma wannan ba dalili ba ne ka shiga cikinsu. An kira ka zama daban. Za ka fuskanci ƙalubale za ka fuskanci tsanantawa, amma idan ka riƙe Allah, za ka yi nasara,” in ji shi.
Babban Fasto ɗin ya ƙara tunatar da jama’a cewa Allah ya riga ya bayyana cewa zai zo nan ba da jimawa ba da ladansa ga kowa, gwargwadon ayyukansu.
Don haka ya yi kira ga Kiristoci da su rayu cikin adalci a ofisoshinsu, kasuwanninsu, sana’o’insu, makarantu da gidajensu, kuma kada su taɓa yin sulhu da masu aikata mugunta, komai matsin lamba ko jarabawar da za su fuskanta.
“Allah yana kallo. Zai zo nan ba da jimawa ba da ladansa. Don haka, ku rayu cikin adalci duk inda kuke. A ofis, kada ku karɓi cin hanci. A kasuwa, kada ku yi ha’inci. A matsayinku, kada ku zalunci wasu. Kada ku yi sulhu da masu aikata mugunta,” in ji shi.
A wani ɓangare mai jan hankali na wa’azin da ya sa jama’a suka yi tafi, Fasto Makpa yace idan aka ba shi damar zama Shugaban Najeriya na tsawon sa’o’i biyu kacal, tabbas zai canza abubuwa ta hanyar gyara su.
A cewarsa abin da zai fi ba da fifiko shi ne yaƙi da zalunci da danniya daga mutanen dake manyan muƙamai da kuma sauran munanan ɗabi’u dake cigaba da talauta al’umma da rarraba ta.
“Idan aka ba ni sa’o’i biyu kacal a matsayin shugaban wannan ƙasa, zan gyara abubuwa yadda ya kamata. Zan yaƙi zalunci da danniya daga sama. Zan yaƙi munanan ɗabi’u dake lalata wannan ƙasa. Shugabanci game da adalci da gaskiya ne,” in ji shi.
Ya jaddada cewa matsalar Najeriya ba rashin albarkatu ko ra’ayoyi ba ne, sai dai rashin shugabanni masu tsoron Allah waɗanda ke shirye su yi abin da ya dace ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
Wakilinmu a jihar ta Nasarawa John D. Wada ya kuma ruwaito cewa sujadar ta kasance mai daɗi kuma cike da ruhu, tare da waƙoƙi masu ratsa zuciya daga ƙungiyoyi daban-daban a cikin cocin ciki har da mawaƙa, matasa, mata da maza.
Sauran abubuwan da suka gudana sun haɗa da rakiyar aure, bikin suna, addu’o’i na musamman ga iyalai, coci, Jihar Nasarawa da Najeriya, da kuma godiya.
Membobin da aka tattauna dasu bayan hidimar sun bayyana wa’azin a matsayin mai dacewa da lokaci kuma mai ƙarfafawa da suka ce kira ne na farkawa ga Kiristoci su tsaya tsayin daka a bangaskiyarsu duk da kalubalen tattalin arziki da ɗabi’a da ƙasa ke fuskanta.
