EFCC za ta binciki Kwankwaso kan zargin mallakar kadarori a Abuja, Kano da Nasarawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta tabbatar wa wata ƙungiyar fararen hula cewa za ta duba ƙorafin da aka shigar gabanta, wanda ke neman a gudanar da bincike kan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa zargin mallakar wasu manyan kadarori a sassa daban-daban na ƙasar.

ƙorafin na neman a tabbatar da ko mallakar kadarorin da ake dangantawa da tsohon gwamnan ta yi daidai da halastattun kuɗaɗen shigarsa da kuma kadarorin da ya bayyana a lokacin da yake riƙe da muƙaman gwamnati.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa hukumar ta bayar da wannan tabbaci ne a ranar Talata, lokacin da ta karɓi ƙorafin da ƙungiyar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Inganta Kyakkyawan Shugabanci (SACGGI) ta miƙa a hedikwatarta da ke Abuja.

ƙungiyar, wadda ta gudanar da zanga-zanga kafin miƙa ƙorafin, ta buƙaci EFCC ta binciki tushen kuɗaɗen da ake zargin an yi amfani da su wajen mallakar kadarorin da ake dangantawa da tsohon gwamnan a Abuja, Kano da Jihar Nasarawa.

Masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin mai magana da yawun ƙungiyar, Muhammad Abdullahi, sun buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan kadarorin, asusun bankuna, bayanan haraji da kuma bayanan kadarorin da Kwankwaso ya bayyana.

Da yake mayar da martani a madadin Shugaban EFCC, Shugaban Ma’aikata na hukumar, Michael Nzekwe, ya ce hukumar za ta yi la’akari da ƙorafin bisa cancantarsa, tare da gudanar da aikinta cikin ƙwarewa.

Ya ce, “EFCC ba ta da alaƙa da siyasa. Ba mu goyon bayan wata jam’iyya. Abin da muke yi kawai shi ne tabbatar da cika nauyin da aka ɗora wa hukumar. Mun ga abubuwan da kuka gabatar, kuma hukumar za ta duba su bisa cancantarsu tare da gudanar da aikinta cikin ƙwarewa.”

Nzekwe ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa za a miƙa ƙorafin ga shugabancin hukumar domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya kuma yi alƙawarin cewa za a ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa, tare da jaddada ƙudirin EFCC na yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifukan kuɗi.

Tun da farko, Abdullahi ya bayyana cewa ƙorafin ya biyo bayan nazarin da ƙungiyar ta gudanar kan rayuwar wasu ’yan siyasa da kadarorin da ake zargin suke da su, gabanin babban zaɓen 2027.

Ya bayyana SACGGI a matsayin ƙungiya mai zaman kanta, wadda ba ta goyon bayan wata jam’iyya, kuma ba ta neman riba, wadda manufarta ita ce inganta riƙon amana da shugabanci nagari.

A cewarsa, ƙungiyar na ganin cewa ya kamata a riƙa yi wa masu riƙe da muƙaman gwamnati tambayoyi kan kadarorinsu da mu’amalolinsu na kuɗi, ba tare da la’akari da matsayinsu na siyasa ba.

Abdullahi ya ce, “Mu matasa ƙwararru ne — lauyoyi, akawunta, injiniyoyi, ’yan jarida da shugabannin al’umma — waɗanda suka yi imani cewa riƙe da muƙamin gwamnati amana ce da jama’a suka ba mutum, kuma babu wanda ya fi ƙarfin doka.”

A cikin ƙorafin, ƙungiyar ta lissafa wasu kadarori da ta ce ana zargin suna da alaƙa da Kwankwaso, tare da neman EFCC ta gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da ainihin masu mallakarsu da matsayinsu.

Daga cikin kadarorin da aka lissafa akwai Key Science Academy da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi, a Masaka, Jihar Nasarawa, da tsohon hedikwatar jam’iyyar NNPP da ke lamba ta 1, Mahatma Gandhi Street, Area 11, Abuja.

Sauran sun haɗa da Plot 3060, CZ A06, da ke Maitama, Abuja; tsohon otal ɗin Clintonia da ke Apo, Abuja; Tidbe Plaza da ke Central Business District; da wani gini da ke lamba ta 10, Port Harcourt Crescent, Area 11, Garki.

Haka kuma, ƙorafin ya ambaci lamba ta 28, Katsina Ala Crescent, Maitama; Makarantar Nigeria-Egypt International School da ke Gwarinpa Estate, Abuja; Kano Mansion da ke Milla Road, Kano; da Hafsat Plaza da ke Constitution Aɓenue, Abuja.

Sai dai SACGGI ta amince cewa ta gano waɗannan kadarori ne ta hanyar rahotannin da aka wallafa a bainar jama’a, tana mai cewa ya kamata EFCC ta gudanar da nata binciken domin tabbatar da masu mallakarsu da ainihin matsayinsu.

ƙungiyar ta kuma yi tambaya kan ko yadda ake zargin aka mallaki kadarorin ya yi daidai da halastattun kuɗaɗen shigar Kwankwaso, da kuma ko an bayyana su yadda ya kamata a lokacin da yake aikin gwamnati.

Tsohon gwamnan ya riƙe muƙamin Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta ƙasa daga 1992 zuwa 1993, sannan ya zama Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015. Ya kuma riƙe muƙamin Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007, sannan ya wakilci Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.

Haka kuma, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a babban zaɓen 2023.

A cikin buƙatunta, SACGGI ta nemi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar ta gudanar da binciken yanayin rayuwar tsohon gwamnan, tare da duba bayanan kadarorin da ya gabatar wa Hukumar Kula da ɗa’ar Ma’aikatan Gwamnati (CCB) daga 1999 zuwa yanzu.

Ta kuma buƙaci a gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan asusun bankuna da bayanan haraji da suka dace, domin gano tushen kuɗaɗen da ake zargin an yi amfani da su wajen mallakar kadarorin.

ƙungiyar ta ƙara buƙatar EFCC ta tabbatar da mallakar kadarorin ta hanyar Hukumar Kula da Tsarin Bayanai na Filaye ta Abuja (AGIS), Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA), hukumomin kula da filaye na Jihar Kano da Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC).

Haka kuma, ta nemi hukumar ta gayyaci Kwankwaso domin yi masa tambayoyi idan buƙatar hakan ta taso, tana mai jaddada cewa ya kamata a ba shi damar kare kansa da kuma yin bayani kan zarge-zargen bisa ƙa’idojin adalci da sauraron ɓangarorin da abin ya shafa.

Masu zanga-zangar sun kuma buƙaci EFCC ta haɗa kai da sauran hukumomin da suka dace, ciki har da CCB, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC), Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (FIRS) da Hukumar Leken Asiri kan Kuɗaɗen Haramtacciyar Hanya (NFIU).

Sun kuma buƙaci hukumar ta gurfanar da duk wanda aka samu da laifi, tare da kwato duk wani kuɗin gwamnati da aka tabbatar an karkatar ko aka yi amfani da shi ba bisa ƙa’ida ba.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta buƙaci a bayyana sakamakon binciken ga jama’a kafin babban zaɓen 2027.

A cikin ƙorafin, ƙungiyar ta ce, “Wannan zanga-zanga ba ta samo asali daga ƙiyayya ko yunƙurin farautar wani saboda siyasa ba. An yi ta ne saboda muradin tabbatar da cewa yayin da Nijeriya ke shirin tunkarar shekarar 2027, mutane masu sahihanci da aka tabbatar da nagartarsu ne kawai za su nemi manyan muƙaman ƙasa. Riƙe da muƙamin gwamnati amana ce da jama’a suka bayar.”

Ta ƙara da cewa, “Idan an mallaki waɗannan kadarori ta hanyar halastacciya, bai kamata ɗan takarar ya samu wata matsala wajen tabbatar da tushen kuɗaɗen da aka yi amfani da su ba. Idan kuwa ba haka ba ne, to doka ta yi aikinta ba tare da la’akari da matsayin siyasar mutum ba.”

SACGGI ta buƙaci EFCC ta gudanar da binciken cikin adalci, ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, tana mai cewa matakin da ta ɗauka ya samo asali ne daga buƙatar inganta riƙon amana da tabbatar da cewa ana ɗora wa masu riƙe da muƙaman gwamnati ma’aunin gaskiya da bayyana kadarori iri ɗaya.

Ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Kwankwaso ba, kuma miƙa ƙorafin ba yana nufin an tabbatar da aikata wani laifi daga gare shi ba.

By ukarofi

Leave a Reply