Yadda ‘yan kasuwa suka yi asarar biliyoyin Naira a gobarar kasuwar kifi ta Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata gobara da ta tashi a kasuwar sayar da kifi da ke kan titin Zariya a cikin birnin Kano, ta lalata shaguna sama da 100, tare da janyo asarar dukiyoyi da ake hasashen sun kai biliyoyin nairori.

Gobarar, wadda ta tashi da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Lahadi, ta bazu zuwa sassa daban-daban na kasuwar da ke kusa da tashar motocin Kano Line, inda ta ƙone shaguna, kwantenoni da kayayyakin ’yan kasuwar. Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta shafi kusan shaguna 150 da kwantenoni 200, yayin da wasu ’yan kasuwa suka yi asarar hajojin da darajarsu ta kai miliyoyin nairori.

ɗaya daga cikin ’yan kasuwar da gobarar ta shafa, Usman Sani, ya bayyana yadda wutar ta bazu cikin kasuwar, tana lalata shaguna da kayayyaki kafin ’yan kasuwar su samu damar kwashe hajojinsu. Ya ce, “Mun samu labarin tashin gobarar, nan take muka garzaya kasuwar, amma kafin mu iso, tuni wutar ta bazu sosai. Gobarar ta shafi shaguna da dama, kuma ’yan kasuwa sun yi asarar kayayyakin da darajarsu ta kai miliyoyin nairori. Lamarin ya karya mana zuciya matuƙa.”

Shi ma wani ɗan kasuwa, Musa Inuwa, ya bayyana gobarar a matsayin babban koma-baya ga mutanen da rayuwarsu ta dogara kacokan kan sana’ar da suke gudanarwa a kasuwar. Ya ce, “Da yawa daga cikinmu sana’ar nan ce kawai muke dogaro da ita wajen ciyar da iyalanmu. Mun rasa hajojinmu da jarinmu, kuma a yanzu ba mu san ta inda za mu fara ba. Muna kira ga gwamnati da ta kawo mana ɗauki.”

’Yan kasuwar da abin ya shafa sun roƙi Gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kai musu ɗauki, domin tallafa wa waɗanda suka rasa shaguna, hajojinsu da jarin sana’arsu. Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:58 na dare, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin da gobarar ta tashi. Jami’an hukumar sun isa wurin bayan mintuna huɗu da samun kiran, domin ƙoƙarin shawo kan gobarar da kuma hana ta ci gaba da yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.

A halin yanzu, har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa ta.

By ukarofi

Leave a Reply