Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin ganin ’yan Nijeriya sun samu ingantaccen lantarki. Ministan ya ce matsalolin da suka shafi rashin kyakkyawar fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki, gazawar shugabanci da matsalolin kasuwanci ne ke haddasa kashi 80 cikin 100 na matsalolin da suka addabi ɓangaren wutar lantarki a ƙasar, yayin da matsalolin fasaha ke da kaso 20 cikin 100 kacal.
Tegbe ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise News a ranar Litinin, inda ya yi bayanin manyan ƙalubalen da ke addabar ɓangaren samar da wutar lantarki da kuma matakan da Gwamnatin Tarayya ke shirin ɗauka domin magance su. Daga cikin matakan akwai sauya tsofaffin kayan aiki da gine-ginen samarwa da rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar.
Ministan ya ce tun bayan hawansa muƙami, binciken da ya gudanar ya ƙara tabbatar masa da sahihancin wannan matsaya tasa. Ya bayyana cewa matsalolin sun mamaye kusan kowane mataki na tsarin samar da wutar lantarki, kuma wasu daga cikinsu sun samo asali ne tun shekaru 50 da suka gabata. Ya lissafa rashin haɗin kai tsakanin masu gudanar da ayyukan wutar lantarki, rashin daidaito a harkokin gudanarwa, matsalolin kuɗaɗen shiga da rashin wadataccen jari, da kuma gazawar shugabanci a matsayin wasu daga cikin manyan dalilan da ke kawo cikas ga samar da wutar lantarki a ƙasar. “Na sha faɗa cewa kashi 20 cikin 100 na matsalar ɓangaren wutar lantarki matsalar fasaha ce, yayin da kashi 80 cikin 100 ke da nasaba da mutane,” inji shi.
Tegbe ya bayar da misalin hasumiyoyin da ake rataya wayoyin lantarki a kansu, waɗanda har yanzu suke ɗauke da tambarin tsohuwar Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (ECN), wadda ta wanzu kafin kafa Hukumar Kula da Samar da Wutar Lantarki ta ƙasa (NEPA). A cewarsa, hakan na nuna irin tsufan kayayyakin more rayuwa da ɓangaren ke fama da su. Ya kuma danganta wasu matsalolin da ake fuskanta da munanan shawarwarin zuba jari da gwamnatocin baya suka riƙa yankewa bisa la’akari da muradun siyasa, maimakon buƙatun fasaha da na al’umma.
A sakamakon haka, a cewarsa, an riƙa girka tiransifoma a wasu al’ummomi ba tare da samar da layukan wutar lantarki da za su kai musu wuta ba. “Idan muka yi la’akari da ɓangaren fasaha, zan gaya muku cewa babbar matsalar ita ce yadda muka riƙƙ kashe kuɗi a kan abubuwan da ba su dace ba,” inji ministan. “Ba mu riƙa ba wa ayyuka fifiko yadda ya kamata a baya ba. Wasu daga cikin shawarwarin da gwamnatocin baya suka yanke sun samo asali ne daga dalilan siyasa.”
Ministan ya ce a halin yanzu ma’aikatarsa na nazarin ayyukan wutar lantarki da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar, domin tantance waɗanda suka fi muhimmanci, gano yadda suke da alaƙa da juna, da kuma tabbatar da waɗanda za su taimaka wajen inganta samar da wutar lantarki ga ’yan Nijeriya. Ya bayyana cewa an riga an kafa wata tawaga da ke gudanar da wannan aiki, domin tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen aiwatar da ayyukan da za su kai wutar lantarki ga jama’a, maimakon zuba jari a ayyukan da ba za su magance ainihin buƙatun ƙasar ba.
Tegbe ya amince da irin wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta a duk lokacin da wutar lantarki ta katse, musamman a lokutan tsananin zafi. Ya ce gwamnati na fahimtar ƙorafe-ƙorafen jama’a, tare da sanin cewa samun wutar lantarki ba batun kasuwanci kawai ba ne. “Bari in gaya muku, a matsayina na Ministan Wutar Lantarki a yau, na fahimci irin azabar da ’yan Nijeriya ke sha. Na fahimci halin da kuke ciki. Idan mutum yana gida babu wutar lantarki, rana na zafi, ga kuma tsananin zafin da ke cikin gida, yana da cikakken ’yancin yin ƙorafi,” inji Tegbe. “A ganina, samar da wutar lantarki ba ciniki kawai ba ne. Haka kuma akwai nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati na kula da jin daɗin al’umma.”
Ministan ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ma yana sane da damuwar ’yan Nijeriya game da matsalar rashin tabbatacciyar wutar lantarki, kuma gwamnati na ƙoƙarin ganin ta shawo kan lamarin. “Muna tattauna wannan batu, kuma muna yin iya ƙoƙarinmu,” inji ministan.
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da cewa talakan Nijeriya ya samu damar amfani da wutar lantarki. “Duk da haka, za mu yi duk abin da ya kamata domin ganin talakawan Nijeriya sun samu wutar lantarki,” inji shi.
Wannan furuci na ministan na zuwa ne makonni kaɗan bayan bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta fara sauya tsofaffin kayayyakin more rayuwa da ke cikin tsarin lantarkin ƙasa cikin wata ɗaya zuwa biyu masu zuwa.
A ranar 9 ga Nuwamba ne ya bayyana shirin, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar wutar lantarki da ta daɗe tana addabar ƙasar.
