Kasashen Amurka, Mexico, Costa Rica da Jamaica ne za su karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta mata ta shekarar 2031, yayin da Ingila, Arewacin Ireland, Scotland da Wales za su haɗa kai wajen karɓar baƙuncin gasar ta shekarar 2035.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ce ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, yayin Babban Taron Gaggawa na hukumar da aka gudanar a birnin Zurich na ƙasar Switzerland. ƙasashen biyu sun samu damar karɓar baƙuncin gasannin ne bayan wakilan ƙasashe mambobin FIFA sun amince da tayinsu ba tare da hamayya ba.
Wannan mataki na nufin cewa gasannin cin kofin duniya na mata guda biyu masu zuwa za su gudana ne a ƙasashe huɗu-huɗu, lamarin da zai ƙara faɗaɗa wuraren da ake gudanar da wannan gasa mai muhimmanci a duniya.
Gasar ta 2031 za ta kasance karo na farko da ƙasashe huɗu za su haɗa kai wajen karɓar baƙuncin gasar kofin duniya ta mata. Haka kuma, za a faɗaɗa yawan ƙungiyoyin da za su fafata zuwa 48, inda za a buga wasanni 104.
Gasar kofin duniya ta mata ta 2031 za ta kasance ta farko da za a gudanar a ƙasashe huɗu, waɗanda suka haɗa da ƙasashen Arewacin Amurka, Amurka ta Tsakiya da kuma yankin Caribbean.
Wannan shi ne karo na uku da Amurka za ta karɓi baƙuncin gasar, bayan da ta yi hakan a shekarun 1999 da 2003. Sai dai ga Mexico, Costa Rica da Jamaica, wannan ne karon farko da za su karɓi baƙuncin babbar gasar kofin duniya ta mata ta FIFA.
Za a faɗaɗa gasar zuwa ƙungiyoyin ƙasashe 48, sabanin ƙungiyoyi 32 da suka fafata a gasar shekarar 2023 da aka gudanar a Australia da New Zealand.
Jimillar wasanni 104 za a buga a gasar, wanda hakan zai sanya ta zama mafi girma a tarihin gasar ta fuskar yawan ƙungiyoyin da za su fafata da kuma adadin wasannin da za a gudanar.
Hukumar ƙwallon ƙafar Amurka ce ta jagoranci shirin neman karɓar baƙuncin gasar, tare da haɗin gwiwar hukumomin ƙwallon ƙafa na Meɗico, Costa Rica da Jamaica.
Ana sa ran ƙasashen huɗun za su yi aiki tare da FIFA da kuma Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Arewacin Amurka, Amurka ta Tsakiya da Caribbean (CONCACAF), domin gudanar da gasar cikin nasara tare da samar da kyakkyawan tasiri mai ɗorewa ga ci gaban ƙwallon ƙafar mata a yankin.
Bisa bayanan shirin neman karɓar baƙuncin gasar da Hukumar ƙwallon ƙafar Amurka ta fitar, ana kuma sa ran wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen ƙara zuba jari a ƙwallon ƙafar ’yan mata, horas da masu horar da ’yan wasa da kuma bunƙasa gine-ginen da suka shafi wasanni.
A wani ɓangaren kuma, Ingila, Arewacin Ireland, Scotland da Wales ne za su haɗa kai wajen karcar baƙuncin gasar kofin duniya ta mata ta shekarar 2035.
Wannan hukunci zai sanya Birtaniya ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta FIFA a karon farko tun bayan da Ingila ta karɓi baƙuncin gasar ta maza a shekarar 1966.
Haka kuma, wannan ne karon farko da Birtaniya za ta karɓi baƙuncin babbar gasar cin kofin duniya ta mata, wadda aka fara gudanarwa a shekarar 1991.
