Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu
Ƙungiyar ’yan Jarida ta ƙasa reshen Jihar Yobe (NUJ), ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanninta da za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa, inda Alhassan Sule Mamudo ya samu nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar bayan samun gagarumar nasara a zaɓen da aka gudanar akan abokan takarar sa a ranar Asabar 28/11/2026.
Wannan zaɓen dai an gudanar da shi ne a sakatariyar ’yan jarida ta NUJ da ke Damaturu.
Kamar yadda sakamakon zaɓen ya nuna, sabon shugaban da ya kai ga kashe zaɓen Alhassan Sule Mamudo ya samu nasarar samun ƙuri’u kimanin 199, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da suka haɗa da Usman Mohammed Nasoro, wanda ya samu kuri’u 14 da kuma Suleiman Mohammed Gambo Bakoro da ya tashi da ƙuri’u 8.
Ita kuwa kujerar mataimakin shugaban ƙungiyar kuwa, Usman Ibrahim Geidam na Sahel Treasure Chapel ne ya yi nasara da kuri’u 181, inda ya kayar da abokin takararsa, Usman Nasidi na majalisar dokokin jihar Yobe State House of Assembly Chapel, wanda ya samu ƙuri’u 33.
Zaɓen sauran muƙamai biyar na shugabancin ƙungiyar an gudanar da shi ne babu hamayya inda dukkan ’yan takarar da aka amince da su suka samu damar lashe zaɓen ba tare da samun wata tangarɗa ba.
Sabbin shugabannin da suka ci babu hamayya sun haɗa da Abdulaziz Mohammed Shehu na gidan talabijin na jiha (YTV) Chapel a matsayin Sakatare; Ahmed Isah Abba na ƙungiyar wakilan kafofin yaɗa labarai (Correspondents Chapel) a matsayin mataimakin sakatare.
Haka nan shi kuma Mohammed Dala Lawan na gidan rediyon Sunshine FM Chapel a matsayin mai binciken kuɗi (Auditor); Yusuf Bukar Biriri na gidan rediyon jiha (YBC) Chapel a matsayin ma’aji; sai Aliyu Mohammed Babi na gidan talabijin na ƙasa (NTA) Chapel a matsayin sakataren kuɗi.
A cikin jawabinsa na godiya bayan samun nasarar zaɓensa, sabon shugaban ƙungiyar, Alhassan Sule Mamudo, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga mambobin ƙungiyar bisa irin gagarumar amincewar da suka nuna masa ta hanyar zabensa da kyakkyawan rinjaye.
Sabon shugaban ya yi alƙawarin gudanar da shugabanci bisa gaskiya, riƙon amana da adalci, tare da tabbatar da haɗin kai, ƙwarewa a aikin jarida da kuma inganta jin dadin walwalar ’yan jarida a faɗin jihar Yobe gaba ɗaya.
Mamudo ya buƙaci dukkan mambobin ƙungiyar da su ba sabon shugabancin goyon baya da haɗin kai, yana mai jaddada cewa samun ci gaba mai ma’ana a cikin ƙungiyar na buƙatar haɗin gwiwa, sadaukarwa da kuma fahimtar nauyin da ke kan kowannensu.
Wannan zaɓen dai ya gudana ne karkashin kulawar hedikwatar ƙungiyar NUJ ta kaysa, inda sakataren shiyyar Arewa maso Gabas, Abubakar Waziri, ya wakilci shugaban ƙungiyar na ƙasa.
Jim kaɗan da kammala zaɓen ne aka miƙa takardun shaidar nasara ga sabbin shugabannin da aka zaɓa a wannan zaɓe da aka gudanar, yadda mambobin ƙungiyar daga kowane yanki na jihar suka samu damar halarta.
