‘Yan bindigar da ake zargin IS ne sun yi garkuwa da wani ɗan ƙasar Saudiyya a Nijar

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Harkokin tsaro a yankin Sahel na ci gaba da fuskantar sabon ƙalubale, bayan wasu ‘yan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar IS sun yi garkuwa da wani ɗan ƙasar Saudiyya a Jamhuriyar Nijar.

Wani rahoton Reuters na ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, ya bayyana cewa mutanen sun yi garkuwa da mutumin ne a ƙarshen makon da ya gabata, kuma har zuwa wannan lokacin ana ci gaba da tsare shi a hannunsu.

Majiyoyin tsaro biyu ne suka tabbatar da faruwar lamarin, inda ɗaya daga cikinsu ya ce sace mutumin ya faru ne a yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar. Yankin yana kusa da iyakokin ƙasar da Mali da Burkina Faso, kuma yana daga cikin wuraren da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi ke gudanar da ayyukansu.

Sai dai wata majiyar ta biyu ta bayyana cewa sace mutumin ya faru ne a wani wuri tsakanin Tillaberi da birnin Yamai, babban birnin Nijar.

Rahoton ya ƙara da cewa ƙungiyar Islamic State Sahel Province ba ta fito ta bayyana cewa ita ce ta kai harin ba. Haka kuma, gwamnatocin Nijar da Saudiyya ba su mayar da martani kan tambayoyin da aka aika musu dangane da lamarin ba.

A yankin Sahel, sace baki da nufin karɓar kuɗin fansa ya zama ɗaya daga cikin hanyoyin da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke amfani da su wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu. Wannan ne ya sa ƙasashen yankin ke fuskantar matsin lamba wajen ƙoƙarin kare fararen hula da kuma baki da ke ziyartar yankunansu.

Lamarin ya sake nuna yadda matsalar rashin tsaro a Sahel ba ta tsaya kan barazana ga al’ummar yankin kawai ba, har ta kai ga sanya rayukan baƙi cikin haɗari.

By ukarofi

Leave a Reply