Paparoma Leo ya nuna damuwa kan gazawar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shugaban Cocin Katolika na duniya, Paparoma Leo XIV, ya nuna matuƙar damuwa kan rashin cimma matsaya a taron ƙasashen duniya kan sauyin yanayi, inda ya yi kira ga shugabannin ƙasashe da su ɗauki matakan da za su taimaka wajen kare duniya daga illolin dumamar yanayi.

Paparoman ya bayyana matsayinsa ne a ranar Laraba, bayan taron Majalisar ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP31 da aka gudanar a Antalya ta ƙasar Turkiyya ya kammala ba tare da samun yarjejeniyar bai ɗaya tsakanin ƙasashen da suka halarta ba.

Rahoton Associated Press ya bayyana cewa rashin cimma matsayar ya samo asali ne daga saɓanin ra’ayoyi tsakanin ƙasashe, musamman kan batun amfani da makamashin burbushin halittu, wanda ya haɗa da man fetur da kwal.

A yayin jawabinsa a filin St. Peter’s Sƙuare da ke birnin Vatican, Leo ya bayyana cewa matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa na ƙara tsananta, inda ake samun aukuwar munanan al’amuran yanayi da suka haɗa da ambaliyar ruwa, fari da sauran bala’o’i.

Ya yi gargaɗin cewa matsalar ba ta shafi muhalli kaɗai ba, domin tana jefa rayukan miliyoyin mutane cikin haɗari, tana lalata al’ummomi, sannan tana barazana ga makomar al’ummomin da za su zo nan gaba.

Paparoman ya yi kira da a samu sauyi a yadda ake tafiyar da al’amuran zamantakewa, tattalin arziki da shugabanci, tare da jaddada cewa kare muhalli nauyi ne da ya rataya a wuyan ƙasashe da kuma kowane mutum.

Tun bayan hawansa kan jagorancin Cocin Katolika, Leo XIV ya ci gaba da jaddada muhimmancin kare muhalli, wanda shi ma ɗaya ne daga cikin batutuwan da magabacinsa, Paparoma Francis, ya fi mayar da hankali a kai.

Rashin cimma yarjejeniya a wannan taro ya sake buɗe tambaya kan yadda ƙasashen duniya za su haɗa kai wajen magance matsalar da masana ke ganin tana ƙara yin barazana ga rayuwar bil’adama.

By ukarofi

Leave a Reply