Shettima ya buƙaci bankuna su rage kuɗin ruwa domin bunƙasa ƙananan sana’o’i

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su sauƙaƙa sharuɗɗan bayar da lamuni, tare da rage kuɗin ruwa, domin ƙarfafa ƙananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu su bunƙasa.

Shettima ya bayyana hakan ne a ƙarshen makon da ya gabata, a Abuja, yayin bikin buɗe sabon babban ofishin shiyya na Bankin Microfinance na Moniepoint da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya wakilta a wajen taron, ya ce wajibi ne cibiyoyin hada-hadar kuɗi su tabbatar da cewa lamunin da suke bayarwa na taimaka wa ’yan kasuwa su bunƙasa, maimakon zama wani ƙalubale da ke kawo cikas ga ci gaban sana’o’insu. Ya bayyana cewa sauƙaƙa lamuni ba wai rage kuɗin ruwa kawai ya ƙunsa ba ne, har da kuɗaɗen hidima, tsawon lokacin biyan bashin da kuma wahala ko tsawon lokacin da mutum ke ɗauka kafin ya samu amincewar lamunin. A cewarsa, duk waɗannan abubuwa ne ke ƙayyade ko lamuni zai taimaka wa sana’ar bunƙasa ko kuma ya jefa mai ita cikin matsin tattalin arziki.

Shettima ya ƙara da cewa bai kamata a takaita manufar bai wa jama’a damar shiga harkokin hada-hadar kuɗi da buɗe asusun banki da amfani da hanyoyin biyan kuɗi kawai ba. Ya ce kamata ya yi a tabbatar da cewa mutane da ’yan kasuwa sun samu damar adana kuɗinsu cikin aminci, gudanar da mu’amalolin kuɗi ba tare da fargaba ba, samun lamunin da ya dace da buƙatunsu da kuma gina sana’o’in da za su dogara da kansu na dogon lokaci. Ya kuma yi kira ga cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su mai da hankali wajen tallafa wa mata ’yan kasuwa, matasa, mazauna karkara da kuma masu gudanar da sana’o’i a wuraren da ba su cikin manyan cibiyoyin kasuwanci.

Dangane da ɓangaren noma kuwa, mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci a samar da lamuni ga dukkan matakan da suka shafi sarƙar samar da amfanin gona, tun daga manoma da masu tattara amfanin gonar, har zuwa masu sarrafa shi, masu jigilar kaya da ’yan kasuwar da ke sayar da amfanin gonar. Ya ce, tsarin bayar da lamunin noma ya kamata ya yi la’akari da yanayin aikin gona, musamman lokutan shuka, girbi da kuma sauyin kasuwa da ka iya shafar ribar manoma.

Shettima ya bayyana cewa manomi na buƙatar lamunin da ya dace da kalandar noman da yake yi, haka kuma mai sarrafa amfanin gona na buƙatar tsarin lamuni da ya yi daidai da lokacin da aikinsa ke ɗauka.

A nasa jawabin, Babban Jami’in Gudanarwa na Bankin Microfinance na Moniepoint, Babatunde Olofin, ya ce bankin na samun damar bayar da lamuni ga ƙananan ’yan kasuwa ne ta hanyar amfani da bayanan mu’amalolin kuɗi da ake tattarawa daga ayyukan biyan kuɗi na zamani da yake gudanarwa.

By ukarofi

Leave a Reply