Kotu ta ba da umarnin daskarar da biliyan N135.58 da ake dangantawa da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja ta bayar da umarnin daskarar da dala miliyan 100, kwatankwacin naira biliyan 135.58, da ake zargin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ke riƙe da su, sakamakon takaddamar da ta taso kan kuɗaɗen mayarwa na Paris Club da kuma kuɗaɗen lauyoyi da masu ba da shawarwari da ake bin su.

Kotun ta kuma umarci bankunan kasuwanci 29 da su bayyana cikin sa’o’i 48 ko ƙungiyar gwamnonin na da asusun ajiya da ke ɗauke da kuɗaɗen da ake takaddama a kansu.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Mai Shari’a O.C. Agbaza ne ya bayar da umarnin wucin gadi na Mareɓa Injunction a ranar 19 ga Nuwamba, bayan wani lauya, Dakta Ted Iseghohi-Edwards, ya shigar da buƙata ba tare da sanar da ɓangaren da ake ƙara ba, kan ƙungiyar NGF da bankunan kasuwanci 29.

Bisa kwafin sahihin umarnin kotun da wannan jarida ta gani a ranar Talata, mai ƙara na neman a biya shi kuɗin bisa wani yarjejeniyar lamuni da ake zargin NGF ta bayar a ranar 20 ga Disamban 2018, a ƙarƙashin wani tsari da gwamnatin tarayya ta biya ƙungiyar dala miliyan 100 domin riƙe su a matsayin mai ruwa da tsaki, har sai an yanke hukunci kan alhakin biyan kuɗaɗen ƙwararru.

Bankunan 29 da aka shigar cikin ƙarar a matsayin waɗanda ake ƙara sun haɗa da Access Bank, Alpha Morgan Bank, Ecobank Nigeria, Fidelity Bank, First Bank, Sterling Bank, United Bank for Africa, Unity Bank, Zenith Bank, Jaiz Bank, Guaranty Trust Bank, Keystone Bank, Stanbic IBTC, Standard Chartered Bank da Wema Bank.

Sauran sun haɗa da Union Bank, First City Monument Bank, Lotus Bank, Paralleɗ Bank, Polaris Bank, Globus Bank, SunTrust Bank, Citibank Nigeria, Noɓa Bank, Optimus Bank, Premium Trust Bank, Signature Bank, Tatum Bank da Titan Trust Bank.

A cikin umarnin, Mai Shari’a Agbaza ya hana NGF, ma’aikatanta, wakilanta da duk wani mai aiki a madadinta cire kuɗaɗen, tura su, karkatar da su, ɓoye su, sayar da su, jingina su ko kuma yin duk wata mu’amala da su.

Kotun ta kuma hana bankunan 29 sakin kuɗaɗen da ke cikin asusun NGF, ko canja wurinsu, cirewa, biyan su ko yin wata mu’amala da su, har zuwa jimillar dala miliyan 100 ko kuma kwatankwacinsu na naira, wato naira 135,580,360,000.

Wani ɓangare na umarnin kotun ya ce: “An bayar da umarnin hana wanda ake ƙara na farko, ko ma’aikatansa, wakilansa ko duk wani mai aiki a madadinsa, cirewa, canja wuri, karkatarwa, ɓoyewa, sayarwa, jingina ko yin wata mu’amala da duk wani kuɗi har zuwa dala miliyan 100 ko kuma kwatankwacinsa na naira, wanda ya kai naira 135,580,360,000.”

Kotun ta bayyana cewa kuɗaɗen sun shafi abin da mai ƙara ke nema bisa yarjejeniyar lamunin da aka ce an bayar a ranar 20 ga Disamban 2018, matuƙar kuɗaɗen suna hannun NGF ko wani mai riƙe da su a madadinta a cikin ikon kotun, har sai an saurari buƙatar umarnin wucin gadi ko kuma kotu ta bayar da wani umarni.

Haka kuma, kotun ta hana bankunan da aka shigar cikin ƙarar sakin, biyan, canja wuri, cirewa, musanya ko karkatar da duk wani kuɗi da ke cikin asusun NGF da ke hannunsu, har zuwa adadin kuɗin da aka ambata.

Mai Shari’a Agbaza ya kuma umarci bankunan da su bayyana cikin sa’o’i 48 bayan an miƙa musu umarnin kotun ko NGF na da asusun ajiya da ke ɗauke da kuɗaɗen da ake takaddama a kansu.

An kuma umarci bankunan da su bayyana lambobin asusun da abin ya shafa, nau’in kuɗin da ke cikinsu, adadin kuɗin da ake da su da kuma kuɗin da suka ajiye bisa umarnin kotun.

Alƙalin ya umarci mai ƙarar da ya gaggauta miƙa takardun fara shari’a, rantsuwar shaida, rubutaccen jawabi, buƙatar umarnin kotu da kuma sahihin umarnin da aka bayar ga waɗanda ake ƙara.

Mai ƙarar ya ce kuɗaɗen nasa ne bisa wata yarjejeniyar lamuni da ake zargin NGF ta bayar, wadda ta yi alƙawarin biyan shi dala miliyan 100 idan aka tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na da alhakin biyan kuɗaɗen ƙwararru da ake bin ta.

Iseghohi-Edwards, wanda ke gudanar da kasuwancinsa da sunan Edwards and Partners Law Firm, ya yi zargin cewa ƙungiyar Incorporated Trustees of the Association of Local Goɓernments of Nigeria (ALGON) ce ta ɗauke shi aiki domin wakiltar ƙananan hukumomi 774 na ƙasar a batutuwan da suka shafi kuɗaɗen mayarwa na London da Paris Club.

Daga bisani, ya shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/856/2016 a Babbar Kotun Tarayya kan gwamnatin tarayya, dangane da kuɗaɗen lauyoyi da shawarwari da ake bin ta sakamakon waɗannan mu’amaloli.

A cewar takardun da ya shigar a kotu, Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 16 ga Fabrairun 2018, inda ta tabbatar da cewa gwamnati na bin sa bashin dala miliyan 318.

Ya ce daga baya gwamnatin tarayya ta biya wani ɓangare na kuɗin, wato dala miliyan 159, ta hanyar takardun Promissory Notes.

Mai ƙarar ya yi iƙirarin cewa hukuncin kotun ya cika sharadin da ke cikin yarjejeniyar lamunin da NGF ta bayar, wanda hakan ya sa ya kamata a biya shi dala miliyan 100 kai tsaye.

Ya kuma yi zargin cewa duk da ya aika wa NGF wasiƙar neman biyan kuɗin a ranar 8 ga Oktoban 2026, ƙungiyar ta ƙi cika alƙawarin da ta ɗauka.

Saboda haka, ya garzaya Babbar Kotun FCT domin neman a kare kuɗaɗen da ake takaddama a kansu har sai an kammala shari’ar da ya shigar.

A yayin neman umarnin wucin gadi, Iseghohi-Edwards ya bayyana fargabar cewa NGF za ta iya tura kuɗaɗen, raba su ko karkatar da su, wanda hakan ka iya kawo cikas ga aiwatar da duk wani hukuncin da kotu za ta yanke a kansa nan gaba.

Ya kuma shaida wa kotun cewa ba zai iya gano takamaiman asusun bankunan da ke riƙe da kuɗaɗen da kansa ba, sai da taimakon umarnin kotu.

Mai ƙarar ya bayar da hujjar cewa umarnin na da muhimmanci domin kare abin da ake takaddama a kansa da kuma hana shari’ar zama aikin banza.

Ya jaddada cewa takunkumin ya shafi adadin dala miliyan 100 ne kawai a matsayin jimilla, ba tare da ninka kuɗin a tsakanin NGF da bankunan da abin ya shafa ba.

An shigar da buƙatar ne bisa tanade-tanaden Dokokin Gudanar da Shari’a na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, musamman Orders 30(3) da 32(1), tare da ikon kotun na musamman.

Yayin da yake amincewa da buƙatar, Mai Shari’a Agbaza ya umarci cewa takunkumin da aka sanya wa bankunan zai ci gaba da aiki har sai an saurari buƙatar mai ƙarar na neman umarnin wucin gadi ko kuma kotu ta bayar da wani umarni.

Alƙalin ya kuma umarci bankunan su shigar da rantsuwar shaida da ke bayyana ko suna da asusun NGF da ke ɗauke da kuɗaɗen da ake takaddama a kansu.

Ana sa ran rantsuwar shaidar za ta bayyana asusun da abin ya shafa, nau’in kuɗin da ke cikinsu, adadin kuɗin da ke akwai a lokacin da aka miƙa musu umarnin, da kuma kuɗin da aka killace, bisa duk wani umarnin sirri da kotun za ta bayar.

An ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga Disamban 2026 domin sauraron buƙatar umarnin wucin gadi.

Sai dai wannan umarni na wucin gadi ne, kuma zargin mai ƙarar kan mallakar kuɗaɗen da kuma alhakin NGF na biyan su na nan a matsayin batun da kotu za ta tantance.

By ukarofi

Leave a Reply