’Yan bindiga sun kashe malamai biyu, sun sace mutum 13 a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga sun kashe malamai biyu tare da yin garkuwa da mutane 13, ciki har da jariri mai watanni 11, a wasu hare-hare daban-daban da suka kai wa al’ummomi a Jihar Zamfara.

Hare-haren, waɗanda suka faru a ƙaramar Hukumar Maru, na daga cikin wasu matsalolin tsaro da aka samu a sassan ƙasar cikin sa’o’i 72 da suka gabata, kamar yadda rundunar ’yan sandan Nijeriya ta bayyana.

A wani harin, ’yan bindigar sun shiga ƙauyen Jabaka, inda suka yi awon gaba da mutane 13, ciki har da jaririn da wasu ƙananan yara.

A wani harin na daban da aka kai a ƙauyen Tungar Janbuzu, ’yan bindigar sun yi wa wasu malamai kwanton ɓauna tare da kashe su yayin da suke aiki a gonakinsu.

An bayyana sunayen malaman a matsayin Kabiru Umar, mai shekaru 35, da Shuaibu Salisu, mai shekaru 35.

Yan sanda sun ce an tura rundunonin musamman, tare da haɗin gwiwar jami’an soji, ’yan sa-kai da mafarauta, domin bin sawun maharan, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.

A wani labarin kuma, jami’an ’yan sanda a Jihar Neja sun kama wani da ake zargi da safarar makamai, mai suna Shehu Adamu, tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda takwas da aka ƙera a cikin gida.

An kama wanda ake zargin a gidansa da ke Gada Oli, Gundumar Wawa, ƙaramar Hukumar Borgu, yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar rundunar ’yan sanda ta yankin da jami’an gadin daji.

Binciken ’yan sanda ya nuna cewa Adamu ya sayi makaman ne daga hannun wani da ake zargi da safarar makamai mai suna Baba Mairiga, daga ƙaramar Hukumar Gummi ta Jihar Zamfara.

Sai dai Mairiga ya tsere, kuma har yanzu ba a kama shi ba.

Wanda aka kama ya amsa cewa yana da alaƙa da wasu abokan harkarsa da suka haɗa da Lawali Maikaji, Salatu Ladan da wani ɗan’uwan Salatu da ba a bayyana sunansa ba.

’Yan sanda sun ce suna ci gaba da ƙoƙarin kama waɗanda suka tsere, tare da gano cikakken tsarin safarar makaman.

A Jihar Taraba kuwa, ’yan sanda sun ƙaddamar da wani samame na haɗin gwiwa da sojoji bayan zargin kashe sojoji biyu da ke aiki a Bataliya ta 93 ta Rundunar Sojin Nijeriya da ke Takum.

Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi wa sojojin kwanton ɓauna tare da harbe su har lahira yayin da suke sintiri na yau da kullum a kan hanyar Dogon Gawa zuwa Katsina-Ala.

An kuma yi zargin cewa maharan sun kwashe bindigogin sojojin kafin su tsere.

An kai gawarwakin sojojin zuwa Babban Asibitin Takum domin gudanar da binciken gawarwaki, yayin da jami’an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen bin sawun maharan da kuma ƙwato makaman da aka sace.

A Jihar Enugu kuwa, ’yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum guda sakamakon harin ’yan daba da jama’a suka kai a yankin Powerline, New Haven, ƙaramar Hukumar Enugu North.

An bayyana mamacin da sunan Godwin, wanda aka kai shi Asibitin Koyarwa na Parklane da ke Enugu, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

A cewar ’yan sanda, wani wanda ake zargi mai suna Nwankwo ya amsa cewa shi da mamacin sun saci wayar hannu da na’urar cajin waya (power bank), lamarin da ake zargin ya haddasa harin da jama’a suka kai musu.

’Yan sanda sun ce ba a kama wani mutum ba dangane da wannan harin da jama’a suka kai, yayin da bincike ke ci gaba.

A Jihar Ogun kuwa, jami’an ’yan sanda sun yi musayar wuta da wasu da ake zargi da fashi da makami bayan samun kiran neman agaji daga al’ummar Larufun.

Jami’an sintiri da sa ido na ’yan sanda, tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na yankin, sun kai ɗauki bayan samun rahoton fashin.

A yayin artabun, maharan sun harbi wani mazaunin yankin mai suna Oluwatimilehin Sotikare, mai shekaru 34, a ƙirji, lokacin da yake ƙoƙarin ceton ’yan’uwansa.

Rahotanni sun ce ’yan fashin sun kuma kwace wayoyin hannu daga hannun wasu mazauna yankin, waɗanda kuɗinsu ya haura naira miliyan 3.9.

’Yan sanda sun ce an kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ’yan fashin ne yayin artabun, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran ’yan ƙungiyar.

Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin sabon rahoton ayyukan rundunar ’yan sanda na sa’o’i 72, wanda ya bayyana matsalolin tsaro da suka haɗa da ayyukan ’yan bindiga, safarar makamai, hare-hare kan jami’an tsaro, tashin hankalin jama’a da fashi da makami a jihohi daban-daban.

By ukarofi

Leave a Reply