FCC ta janye dakatarwar horon ɗaukar aikin Kwastam

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya FCC, ta sanar da ɗage dakatarwar wucin-gadi da ta yi akan harkokin ɗaukar aikin Hukumar Kwastam (NCS) da ya ƙunshi sababbin ɗiba guda 3,852, biyo bayan nazari kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar da shawarwari da ta yi da hukumar gudanarwar NCS.

FCC ta ce, ta tsoma baki a aikin ne sakamakon koken al’umma na cewa akwai al’amuran saɓa wa ƙa’idoji a cikin hanyoyin ɗaukar aikin, ciki har da iƙirarin cewa an maye gurbin wasu da wasu mutane daban da cogen gurabe, lamarin da ya sa hukumar ta hanzarta yin nazari kan rahoton ɗibar aikin da bincike akan ƙorafe-ƙorafen da wasu da suka nemi aikin suka shigar mata.

A wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, 27 ga Nuwamba, 2026 ta hannun Kakakinta, Ademola Lawrence, FCC ta bayyana cewa sakamakon bincikenta ya gano cewa an samu masu neman aikin 317 da al’amarin rashin gaskiya da maye gurbi ya shafa. A cewar hukumar, NCS ta riga ta cire sunayen baki ɗayansu daga jaddawalin waɗanda aka ɗiba.

Hukumar ta ɗage dakatarwar ne bayan mako guda ana zama da gudanar da shawarwari da hukumar gudanarwar kwastam, inda ta ƙara da cewa za ta cigaba da sanya ido akan sauran matakan ɗaukar aikin domin tabbatar da biyayya ga hukunce-hukuncen ɗa’ar ma’aikata na tarayya.

Ta kuma sanar da cewa, za ta bayar da ƙarin bayani kan dalilan da suka haifar da zargin rashin gaskiya, wanda za ta gabatar tare da NCS a yayin taron manema labarai a ranar 30 ga Nuwamba, 2026.

Kazalika, hukumar ce jimillar ‘yan Nijeriya 576,000 ne suka nemi aikin, yayin da 3,852 suka yi nasarar zuwa matakin jaddawalin ƙarshe. Daga bisani an cire mutum 505 kan rashin cancanta ko soke sunayensu daga sauye-sauyen jaddawali bisa wasu dalilai, ciki har da 126 da aka sallama bisa faɗuwa a gwajin ƙwaya, takardun shaida na bogi da kuma matsalolin shekeru. Akwai kuma 62 da ba su je wajen karɓar horo ba.

FCC ta bayyana cewa, ta ɗauki matakin tsoma baki cikin al’amarin ne domin tabbatar gaskiya da adalci da tabbatar wa waɗanda suka cancanta daga ko’ina a faɗin ƙasar an mu’amalnce su kamar kowa a kowane matakin ɗibar ma’aikatan.

By Babaji

Leave a Reply