Masarautar Fika ta nemi Mallam Wali ya warware batun iyakarta da masarautar Potiskum idan ya zama gwamnan Yobe

Spread the love

Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu

Masarautar Fika mai hedikwata a garin Potiskum cikin jihar Yobe, ta roƙi ɗan takarar gwamnan jihar Yobe ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC, Alhaji Baba Mallam Wali, da ya warware batun iyakokin Masarautun Fika da Potiskum a cikin garin Potiskum in ya zama gwamnan jihar a zaɓen da ke tafe na 2027.

Masarautar ta bakin mai magana da yawun masarautar Barista Babakura Ba’aba Abba Zarma kuran yayin ziyarar gaisuwar da Baba Mallam Wali ya kai wa Mai Martaba Sarkin Fika a fadarsa da ke Potiskum.

A cewar Barrister Baba Kura Ba’aba, Zarman Kuran Fika ta kasance hedikwatar Masarautar Fika tun shekarar 1913, yayin da Yerimaram kuma ta kasance hedikwatar Masarautar Pataskum.

Ya ƙara da cewa, a halin yanzu, masarautun biyu kowannensu yana da gundumomi shida a Potiskum, amma har yanzu ba a fayyace iyakokin ikon gargajiya na kowace masarauta yadda ya kamata ba.

Don haka masarautar ta buƙaci Baba Mallam Wali in ya zama gwamnan da ya yi amfani da ikon gwamnati wajen ayyana iyakokin gundumomin masarautun biyu domin kare mutuncinsu, hana rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya tsakanin juna.

A cewar sa masarautar ta Fika na jaddada cewa batun yana buƙatar hukunci bisa doka da tsarin gudanarwa, ba muhawarar siyasa ba.

A cikin jawabinsa, Baba Malam Wali ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya umurce shi da ya ziyarci dukkan masarautun da ke cikin jihar a matsayin wani bangare na shawarwarin da yake yi da masarautun gargajiya.

Ya bayyana godiyarsa ga kyakkyawar dangantakar aiki da yake da ita tare da Mai Martaba Sarkin Fika kuma ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta neman albarkar sarakuna, iyayen ƙasa da kuma goyon baya.

Dan takarar jam’iyyar APC ya yi kira ga sarakuna iyayen ƙasa da kuma mutanen jihar da su goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyyar APC a dukkan matakai, inda ya bayar da hujjar cewa ci gaba da jituwa ta siyasa da gwamnatin tarayya zai haifar da ƙarin damammaki ga Jihar Yobe.

Wali ya jinjinawa gwamnatocin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Tinubu, musamman kan ƙoƙarin da suka yi na inganta yanayin tsaro, kuma ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa, idan an zaɓe shi, za ta yi aiki don inganta jin dadi da ci gaban masarautun.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kasance ƙarƙashin jagorancin manufa da kuma ƙa’idojin ci gaba, haɗa kai da kuma ƙikire-kirƙire, tare da gina kan ginshiƙin da gwamnatocin da suka gabata suka shimfiɗa.

By ukarofi

Leave a Reply