Daga JOHN D. WADA a Lafia
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yaba wa masu zaɓe kan natsuwa da kwanciyar hankali da suka nuna yayin atisayen tantancewa da ɗora sakamako na gwaji da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar.
Dr. Nawani Aboki, kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar bayan ya zagaya ya duba yadda atisayen ke gudana a ƙaramar hukumar Doma ta jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa INEC ce ta shirya atisayen domin gwada shirye-shiryen aiki na na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) da kuma shafin duba sakamakon zaɓe na INEC (IReV) gabanin babban zaɓen 2027.
Aboki ya bayyana cewa an gudanar da atisayen a rumfunan zaɓe 294 a cikin mazabu 147 na jihar.
Yace gwamnati ta ji daɗin yadda masu zaɓe suka gudanar da kansu cikin tsari da natsuwa a rumfunan zaɓe daban-daban da suka ziyarta a ƙaramar hukumar Doma.
Ya ce natsuwar da aka gani a yayin atisayen ta nuna cewa al’ummar Jihar Nasarawa sun himmatu ga dimokuraɗiyya kuma sun shirya don gudanar da sahihin zaɓen 2027.
“Gwamnati tana yaba wa masu zaɓenmu da suka fito cikin natsuwa suka shiga cikin atisayen gwaji. Wannan alama ce ta balaga da shirye-shirye don babban zaɓen 2027,” in ji Aboki.
Kwamishinan ya ƙara bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta gudanar da wayar da kan mazauna jihar ta hanyoyi daban-daban domin ƙarfafa su su shiga cikin atisayen.
Ya ce wasu daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka sun haɗa da fassara saƙonnin INEC zuwa Hausa da sauran manyan harsunan asali, domin tabbatar da cewa al’ummomin karkara sun fahimci tsarin zaɓe.
Aboki ya ce gwamnati ta shirya tallace-tallacen rediyo a Turanci, Hausa da harsunan gida da kuma sanarwar hidimar jama’a da ke lissafa rumfunan zaɓe 294 da aka zaɓa don atisayen a jihar.
Kwamishinan ya ce manufar amfani da harsuna da dama ita ce cire shingen harshe da tabbatar da cewa saƙon ya isa ga kowane ɓangare na al’umma, musamman al’ummomin karkara.
Aboki ya kuma gode wa jami’an tsaro, manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar da suka taka wajen tabbatar da gudanar da zaɓen gwaji cikin kwanciyar hankali a jihar.
Haka kuma da yake magana da manema labarai, Nehemiah Anji, Shugaban Rumfar Zaɓe a Akabe Junction, Mazabar Galadima, ƙaramar hukumar Doma, ya bayyana atisayen a matsayin abin burgewa kuma mai natsuwa.
Yace fitowar masu zaɓe ta yi yawa, ya ƙara da cewa ba su samu wata matsala ba da fasahar da aka tura don atisayen.
A halin yanzu wakilin mu ya lura cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurare masu muhimmanci a babban birnin jihar da sauran ƙananan hukumomi domin tabbatar da cigaba da gudanar da zaɓen gwajin ba tare da wata matsala ba a jihar kamar yadda ake gudanar a wasu jihohin ƙasar nan a yanzu haka.
