‘Idan ba ku yi zaɓe ba za mu ɗauki mataki akanku’: Gwamnan Ebonyi ga ‘yan jiharsa kan adawa da APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya yi barazanar hukunta mazauna jiharsa muddin suka ƙi zaɓar jam’iyyar APC a zaɓukan 2027. Nwifuru ya furta haka ne a ƙauyen Amasiri da ke Ƙaramar Hukumar Afikpo ta Arewa, inda ya gargaɗi mazauna akan goyon bayan wata jam’iyya saɓanin mai mulkin.

A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga gwamnan yana faɗa wa wani taron jama’a cewa zai hora su matuƙar ba su zaɓi APC ba. “Idan ba ku zaɓi APC ba, zan hukunta ku. Sai na yi nasara, kuma idan na yi, zan yi maganinku a mafi tsananin salo,” inji shi.

Waɗannan kalamai sun tayar da ƙura musamman a kafafen sada zumunta akan yadda ‘yan siyasa suke wulaƙanta masu zaɓe ta hanyar amfani da ƙarfin mulki su matsa wa ‘yan ƙasa wajen zaɓen wata jam’iyya gabanin zaɓukan 2027. Kalaman Nwifuru na nufin mazauna za su fuskanci juya baya daga ɓangaren gwamnan ta hanyar janye dukkan wasu alfanu da suke samu daga gare shi idan ba su zaɓi APC ba yayin zaɓukan.

A ƙarƙashin dokar Nijeriya, ‘yan ƙasa suna da ‘yancin zaɓar ‘yan takarar da suke so da jam’iyyu a kowane mataki ba tare da wata tsangwama ba. Wannan ɗaya ne kuma na kwanan nan daga cikin ire-iren kalamai masu tayar da ƙura da ‘yan siyasa suke yi wajen barazana ga mazauna kan zaɓinsu gabanin zaɓukan na 2027.

A watan Agusta ne dai aka samu wasu rahotanni daga Jihar Borno da ke nuna cewa Kwamishinan Matasa da Wasannin jihar, Sainna Buba ya yi wa mazauna yankinsu barazanar zane dukkan wanda ya ƙi zaɓar APC a 2027. Daga bisani ya bayar da haƙuri tare da janye kalaman nasa.

Haka ma wani Samuel Shekwolo, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Kuje da ke Abuja, inda aka gan sa a wani bidiyo yana yi wa mazauna barazana kan lallai sai sun zaɓi APC ko kuma su bar yankin. A Jihar Edo, an samu Blessing Ebhodaghe, wato shugaban Ƙaramar Hukumar Esan, wanda ya yi irin wannan barazanar.

Sashe na 97 da Dokar Zaɓe ta 2026, ya haramta wa jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, masu neman takara da ɗaiɗaikun mutane yin barazana ga kowaye akan razanawa da ƙarfi ko rikici yayin yaƙin neman zaɓe don tilasta musu goyon baya ko watsi da wata jam’iyya ko ɗan takara. Dukkan wanda aka samu da hannu a laifin taka dokar, zai biya Naira miliyan 5 ko zaman gidan yari na wata 12, yayin da su kuma jam’iyyu za a ci su tara.

By Babaji

Leave a Reply