
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fara gudanar da gwajin tantance masi zaɓe da ɗora sakamako gabanin zaɓukan 2027, inda aka samu ƙamfar mutane da ƙarancin isar da saƙo ga al’umma a wasu rumfuna.
An gudanar da aikin a ranar Asabar, 27 ga Nuwamba, 2027 a jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja, wanda aka tsara da nufin gwada halin aikin na’urar tantancewa ta Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), raba ma’aikatan zaɓe da kimtsin hukumar ga zaɓukan da ke tafe.
A jihar Borno, wasu rumfunan da wakilinmu ya ziyarta, an ga rashin fitowar jama’a, inda mazauna da dama suka ce ba su da labarin shirin. An samu jinkiri a wasu wurare, ciki har da sassan Jere da Maiduguri babban birnin jihar, inda jami’an tsaro suke je akan lokaci su kuma ma’aikatan INEC suka je a latti.
Wani jami’in hukumar a wata rumfa, ya ce na’urar BVAS tana aiki yadda ya dace saidai an yi aikin ba tare da ita ba a wasu wuraren saboda ƙarancin sabis.
Sauran wuraren da wakilanmu suka ziyarta sun haɗa da makarantun firamare ta Kabuga a Ƙaramar Hukumar Gwale da ta Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso inda aka fara aikin da misalin ƙarfe 10 na safe, saidai ‘yan jarida sun isa wajen kafin ma’aikatan zaɓen.
A Abuja, a Ƙaramar Hukumar Birni (AMAC), mutane da dama ba su samu halarta ba. Wasu mazauna sun ce INEC ta tura musu saƙon gayyata zuwa wajen aikin yayin da wasu suka ce ba su da masaniya a kai kafin lokacin.







