Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA), Jihar Katsina, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani wajen magance matsalolin tsaro, kayan aiki da ƙarancin ma’aikata da jami’ar ke fama da su, tana mai gargaɗin cewa rashin isassun kayan aiki da yawan ɗaliban da ke ƙaruwa na matsa wa jami’ar wajen ba da ilimi mai inganci.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Othman, ya yi wannan roƙon ne a ranar Asabar, a yayin babban taron yaye ɗalibai na haɗe na 10 da 11 na jami’ar, inda ya bayyana rashin isasshen wutar lantarki da ruwa, rashin kyawawan hanyoyin cikin jami’a, ƙarancin ɗakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, ofisoshin ma’aikata da masaukin ɗalibai a matsayin manyan matsalolin da ke damun jami’ar.
Farfesa Othman ya ce ci gaban harabar dindindin (Permanent Campus) na jami’ar ya kasance babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba, yana mai lura da cewa ƙaruwar ɗalibai da faɗaɗar ayyukan ilimi sun ƙara matsa wa kayan aiki a harabar ɗakunan karatu na jami’ar.
“Ɗaya daga cikin matsalolin da suka fi damun jami’ar shi ne ƙaruwar matsin lamba a kan kayan aiki na ɗakunan karatu musamman yayin da yawan ɗalibai da ayyukan ilimi suka faɗaɗa a cikin shekaru,” in ji shi.
Ya bayyana cewa jami’ar ta ɗauki tsarin mataki-mataki na mayar da ayyukan ilimi da na gudanarwa zuwa harabar dindindin, amma ya jaddada cewa tsarin na buƙatar goyon bayan gwamnati domin samar da muhimman kayan aiki da hidimomi.
Shugaban Jami’ar ya roƙi gwamnatin tarayya da ta samar da isasshen wutar lantarki da ruwa, hanyoyin cikin jami’a, ɗakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, ofisoshin ma’aikata, masaukin ɗalibai da kayan aikin tsaro a harabar dindindin.
Ya kuma nuna damuwa kan rashin tsaro da ke shafar cibiyoyin ilimi, musamman a Arewacin Najeriya, yana mai bayyana tsaro a matsayin ginshiƙi ga ikon jami’ar na sauke nauyin da ke kanta.
Farfesa Othman ya bayyana cewa jami’ar ta shirya taron horaswa kan tsaro (security retreat) tare da ƙwararru a fannin tsaro da wakilan hukumomin da abin ya shafa, domin duba tsare-tsaren da ake da su da kuma gano matakan ƙarfafa sa ido, kariyar jiki, shirye-shiryen gaggawa da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi.
Ya ƙara da cewa jami’ar ta ci gaba da tuntuɓar Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Katsina da hukumomin tsaro da abin ya shafa domin inganta tsaron harabobinta da al’ummomin da ke kewaye da su.
Ya yaba da gudunmuwar ma’aikatar ilimi ta tarayya, asusun tallafa wa ilimin manyan makarantu (TETFund), asusun lamunin Ilimi na Najeriya (NELFund) da sauran hukumomi wajen inganta samun ilimi, kayan aiki, ci gaban ilimi da ƙarfin jami’a.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance ƙarancin ma’aikata, ƙarfafa kayan bincike da samar da kayan aikin da ake buƙata domin jami’ar ta yi aiki yadda ya kamata a harabar dindindin.
Ɗalibai fiye dubu 10 suka sami takardar shaidar kammala karatun da suka hada da PHD, digiri na farko da sauran su.
Haka kuma jam’iyar ta karrama tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya Janaral Tukur Burutai da hamshakin ɗan Kasuwa Alhaji Dahiru Ba’rau Mangal da digirin girmamawa kan shari’a da kasuwanci.
