Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyoyin kare haƙƙin mata da yara uku sun ƙaddamar da wani gangamin wayar da kan jama’a domin neman ƙarin kariya ta doka da tabbatar da samun adalci ga mata da ’yan mata a Nijeriya.
Kungiyoyin da suka haɗa kai wajen gudanar da gangamin su ne BAOBAB for Women’s Human Rights, Gidauniyar Kare Yara da Matasa (CYPF), da kuma Gidauniyar Shehu Musa Yar’Adua (SMYF).
Gangamin mai taken “Maputo in a Minute: Justice in Every Space” (Yarjejeniyar Maputo cikin minti ɗaya: Adalci a kowane fage), wani ɓangare ne na ayyukan kwanaki 16 na wayar da kan jama’a kan yaƙi da cin zarafin mata da ’yan mata na shekarar 2026.
Kungiyoyin sun bayyana cewa za su fitar da saƙonnin bidiyo 16, inda shugabanni da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama za su riƙa gabatar da saƙo na daƙiƙa 60 a kowace rana, daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga Disamba.
Manufar gangamin ita ce jawo hankalin jama’a kan giɓin da ke tsakanin alƙawuran da Nijeriya ta ɗauka na kare haƙƙin mata da kuma yadda mata da ’yan mata ke fuskantar cin zarafi, wariya da rashin adalci a gidajensu, wuraren aikinsu, muhallansu da kuma kafafen sadarwa na zamani.
Gangamin na gudana ne ƙarƙashin taken duniya mai cewa: “Mu haɗa kai wajen kawo ƙarshen cin zarafin mata da ’yan mata: A tabbatar da adalci, a kare wazanda aka zalunta, a kawo ƙarshen rashin hukunta masu laifi.”
Kungiyoyin sun gabatar da manyan buƙatu guda uku ga Gwamnatin Tarayya da ’yan majalisun dokoki domin inganta kariya da haƙƙin mata.
Buƙata ta farko ita ce tabbatar da cikakken aiwatar da dokar hana cin zarafin mutane (Violence Against Persons (Prohibition) Act — VAPP) a dukkan jihohin ƙasar.
Sun bayyana cewa duk da cewa jihohi 34 cikin 36 na Nijeriya sun amince da dokar, har yanzu akwai babban gibi wajen aiwatar da ita yadda ya kamata.
A cewarsu, kafa doka kaɗai ba zai wadatar wajen kare waɗanda ake zalunta ba, matuƙar ba a samar da hanyoyin da za su sauƙaƙa musu neman taimako, gudanar da bincike mai inganci, gurfanar da masu laifi da kuma tabbatar da an yi musu adalci ba.
Saboda haka, sun nemi a ƙarfafa hukumomin da ke da alhakin aiwatar da dokar, a samar musu da isassun kayan aiki da tallafi, tare da wayar da kan jama’a domin waɗanda aka zalunta su samu damar neman haƙƙinsu ba tare da fuskantar cikas ba.
Buƙata ta biyu ita ce shigar da yarjejeniyar Maputo cikin dokokin Nijeriya. Yarjejeniyar wadda Tarayyar Afirka ta amince da ita, tana tanadin kare haƙƙin mata a nahiyar.
ƙungiyoyin sun ce Nijeriya ta amince da yarjejeniyar a shekarar 2004, amma har yanzu ba ta shigar da ita cikin dokokin ƙasar yadda ya kamata ba. Sun yi imanin cewa yin hakan zai ƙarfafa tsarin doka na kare haƙƙin mata, tare da bai wa hukumomin gwamnati damar ɗaukar nauyin rashin cika alƙawuran da suka ɗauka.
Yarjejeniyar ta tanadi haƙƙoƙi da dama, ciki har da kariya daga cin zarafi, wariya da munanan al’adun da ke tauye haƙƙin mata.
Buƙata ta uku ita ce amincewa da ƙudirin dokar ware kujeru na musamman ga mata a majalisun dokoki, domin magance ƙarancin wakilcin mata a harkokin siyasa.
Kungiyoyin sun bayyana cewa mata na da kusan kashi huɗu cikin ɗari ne kawai na kujerun Majalisar ƙasa, lamarin da suke ganin yana rage damar mata wajen shiga harkokin yanke shawara da tsara manufofin da suka shafe su.
Sun ce ƙara yawan mata a zaɓaɓɓun muƙaman gwamnati zai taimaka wajen samar da dimokuraɗiyya mai wakiltar kowa, tare da tabbatar da cewa ana la’akari da muradun mata a harkokin mulki.
