Lokacin maida biki ya yi kamar yadda Tinubu ya bai wa Buhari goyon baya a 2015 – Shettima

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci masu zaɓe a Arewa da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027, yana mai bayyana zaɓen mai zuwa a matsayin damar da yankin zai rama goyon bayan siyasar da Shugaban ƙasar ya taɓa ba shi a baya.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Shettima ya yi wannan kira ne yayin rabon kayayyaki da ƙaddamar da wasu ayyukan tallafi na musamman da Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) ta gudanar a Jihar Borno.

Ya tuna cewa Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin babban zaɓen 2015.

A cewar mataimakin shugaban ƙasar, Tinubu ya matsar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar zuwa Legas da gangan, sannan ya tattara goyon baya ga Buhari a yankin Kudu maso Yamma. Ya ce wannan mataki ya taimaka wajen ganin tsohon shugaban ƙasar ya zama ɗan takarar jam’iyyar.

Shettima ya ce: “Mu da muka kasance cikin harkokin siyasa a wancan lokaci, za mu iya shaida cewa ba tare da ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu ba, da Muhammadu Buhari bai samu tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a Legas a 2014 ba.

“Da gangan ya matsar da wurin gudanar da zaɓen fidda gwani zuwa Legas, sannan ya yi ƙoƙari sosai wajen tabbatar da goyon bayan Kudu maso Yamma. Kuma alheri ɗaya yana cancantar a rama shi da wani.”

Ya buƙaci al’ummar Arewa su rama goyon bayan siyasar da Tinubu ya bayar ta hanyar mara masa baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓe, yana mai cewa yankin na da damar rama wannan alheri.

Shettima ya ce: “Mu kuwa a Arewa, lokacin rama alheri ya yi. Ina kira gare ku, ina roƙon dukkanmu da ke nan, mu yi amfani da fahimta da hikimarmu wajen yanke shawarar da za ta amfani ƙasarmu.”

Yayin da yake kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, Shettima ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su yi la’akari da yadda gwamnati ta gudanar da tattalin arziki wajen yanke shawarar wanda za su mara wa baya a zaɓen 2027.

Ya ambaci raguwar hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙarin ajiyar kuɗin waje na ƙasar, wanda ya ce ya kai matsayinsa mafi girma cikin shekaru 17.

Shettima ya ce: “Tattalin arzikin ya fara samun sauƙi. Hauhawar farashin kayayyaki ta ragu. Ajiyar kuɗin wajenmu ta kai matakin da ba a taɓa gani ba cikin shekaru 17 da suka gabata. A yanzu tana kusan dala biliyan 55.”

Da yake kare matakin cire tallafin man fetur, mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba a ɗauki matakin ne da nufin ƙara tsananta wa ’yan Nijeriya wahalar tattalin arziki ba, sai dai domin hana tattalin arzikin ƙasar durƙushewa.

Ya ce: “Shugaban ƙasa yana da matuƙar tausayawa al’ummar Nijeriya. Bai cire tallafin man fetur domin jefa ’yan Nijeriya cikin wahala ba, a’a. Ya cire tallafin ne domin ceton tattalin arzikin Nijeriya daga durƙushewa.”

By ukarofi

Leave a Reply