Rundunar sojoji ta faɗi sunan mai ɗaukar nauyin yaɗa labaran ƙarya kan dakarunta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar sojoji ta bayyana wani mai suna Mista Iliyia Stephen a matsayin jagoran wata ƙungiyar masu zanga-zanga da ake zargi da hannu a ɗaukar nauyin rahotannin da ke adawa da dakarunta na atisayen ENDURING PEACE kan iƙirarin suna da hannu a ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa doka ba a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato. Hedikwatar jami’an haɗaka ta atsayen ta yi watsi da zarge-zargen a matsayin ƙarya kuma mai ruɗarwa, tana mai cewa jami’anta ba su da hannu a wani aikin haƙo ma’adinai ba bisa doka ba a yankin.

Hedikwatar ta yi zargin cewa wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne ba bisa doka ba suka ɗauki nauyin rahotannin, waɗanda suke ganin tura dakarun da aka yi yankunansu takura ce a gare su, inda kuma ta zargi wasu masu zanga-zanga da farmakar jami’an sojoji yayin shiga tsakani a wani gurin da ake shirin fara aikin haƙar ma’adinai.

A sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi ta bakin Kakakinta Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, rundunar ta ce zarge-zargen da ke yawo a kafafen sada zumunta sun sha bam-ban da ainihin abin da ya sa aka tura sojojin zuwa yankin.

Ta ce, an tura jami’an ne a ranar 23 ga Nuwamba a wani guri da ake shirin fara ayyukan haƙo ma’adinai na wani mutum mai suna Mista Pam Bitrus, bayan wani bayanin sirri ya nuna cewa akwai yiwuwar a kai farmaki a yankin. A lokacin da jami’an suka isa wajen sun tarar da masu aikin haƙar sun samu saɓani a tsakaninsu da ya kai ga rikici ya ɓarke tsakanin mai filin da ‘yan yankin kan ayyukan. Sojojin sun shiga tsakani ne da nufin sulhunta ɓangarorin domin kauce wa caɓewar al’amarin, matakin da ya sa aka yi nasarar sulhunta su ta hanyar tattaunawa da taimakon shugaban ƙaramar hukumar.

Saidai, daga bayan an samu wasu matasa da mata sun gudanar da zanga-zanga kan ganin sojoji a yankin tare da nuna buƙatar su fice daga wajen, inda suka zargi sojojin da neman a ba su guri a wajen haƙar ma’adinan wanda ya sa jama’a suka riƙa jifar su da duwatsu da wasu ababe, wanda ya kai ga damejin motar sojoji da raunata guda a kansa.

Akan haka ne rundunar ta gayyaci dukkan jami’an da al’amarin ya shafa domin gudanar da bincike akansu, tana mai kira ga mazauna da su kwantar da hankali da cigaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai da tabbatar musu da ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya a yankunansu.

By Babaji

Leave a Reply