Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar ƙolin Shari’a ga Harkokin Addinin Musulunci ta ƙasa (NSCIA) ta ce ta yi wa Majalisar Zartarwarta ta ƙasa (NEC) garambawul tare da faɗaɗa ta, domin ƙarfafa tsarin gudanarwa da ayyukanta.
Jami’in hulɗa da jama’a na majalisar, Abbas Jimoh, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan wasu shawarwari da aka cimma a Babban Taron Majalisar (General Assembly) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026.
Ya ce taron ya samu halartar shugabannin Musulmi, ciki har da sarakunan gargajiya Musulmi da manyan limaman masallatan Juma’a daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
A cewarsa, Babban Taron ya amince da sabunta tare da faɗaɗa tsarin shugabancin ƙasa na majalisar, inda aka naɗa Farfesa Mahfouz Adedimeji a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na ƙasa, Farfesa Salisu Shehu a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na ƙasa-da-ƙasa, Abeny Mohammed (SAN) a matsayin Mataimakin Babban Sakatare mai kula da harkokin kamfanoni, yayin da Dakta Bala Muhammad ya zama Mataimakin Babban Sakatare mai kula da harkokin gudanarwa.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dakta Umar Jibrilu Gwandu a matsayin Jami’in Hulɗa da Jama’a (PRO) na ƙasa, yayin da Hajia Sekinat Lawal ta zama Mataimakiyar Jami’in Hulɗa da Jama’a (DPRO).
Haka kuma, an naɗa Dakta Mairo Mandara a matsayin Jami’ar Ci Gaba, yayin da aka naɗa Arc. Abdullahi Musa PenAbdul a matsayin Mataimakin Jami’in Ci Gaba mai kula da harkokin fasaha. An kuma naɗa Farfesa Fatimah Abdulkarim a matsayin Jami’ar Harkokin Iyali.
Faɗaɗa tsarin shugabancin na zuwa ne yayin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira da a ƙarfafa fahimtar juna da haƙurin addini a yayin Babban Taron.
Sarkin Musulmin ya ce babu wanda ya kamata a tilasta masa shiga addinin Musulunci, yana mai jaddada cewa ya kamata Musulmi su mutunta ’yanci da haƙƙoƙin mutanen da suke bin sauran addinai.
