Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun mamaye yankin Nasarawa da ke cikin al’ummar Damba, a wajen birnin Gusau na Jihar Zamfara, inda suka kai hari kan mazauna yankin tare da yunkurin satar dabbobi.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne cikin daren Litinin, inda suka mamaye wurare daban-daban masu muhimmanci domin hana yiwuwar samun taimako daga wasu al’ummomin da ke kusa.
Wata mata da ta tsira daga harin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa jaridar cewa ’yan bindigar sun kai farmaki yankin Nasarawa da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka tsallake katanga suka shiga gidanta yayin da suke harbe-harbe ba kakkautawa.
Ta ce: “’Yan bindigar sun kai hari yankinmu da misalin ƙarfe 1:00 na dare, suka tsallake katanga suka shiga gidana, amma Allah Ya cece mu. Daga baya sun fita ba tare da sun cutar da kowa ba, amma harsasai sun bazu ko’ina a harabar gidanmu.”
Wani mazaunin yankin, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar sun shiga yankin da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka rika bi gida-gida suna ƙwanƙwasa ƙofofi tare da tambayar mutanen da suke neman a cikin gidaje.
Ya ce: “Sun bi gida-gida suna ƙwanƙwasa ƙofofi suna tambayar wani mutum da suke nema. Mutanen gida suna gaya musu cewa mutumin da suke nema ba ya nan.
“Daga nan sai suka fara harbe-harbe ba kakkautawa, sannan suka bazu a wurare daban-daban masu muhimmanci.”
Mazaunin ya ƙara da cewa daga baya ’yan bindigar sun karkata hankalinsu wajen satar dabbobi.
Ya ce: “Mun ji suna tattaunawa kan yadda za su sace dabbobi. Wasu daga cikinsu suka ce matsalar ita ce dabbobin suna can gefen babbar hanya. Daga nan sai suka tsallaka zuwa wata makaranta da ke kusa.”
Ya ce daga baya ’yan bindigar sun koma kokarin satar ƙananan dabbobi a yankin Nasarawa, amma daga bisani suka tsere bayan jami’an ’Yan Sanda da mambobin Rundunar Hadin Gwiwar Tsaron Fararen Hula suka isa yankin tare da yi musu arangama.
Mazaunin ya kuma yi zargin cewa ’yan bindigar sun bi ta wani shingen binciken sojoji da ke cikin daji kafin su shiga yankin.
Ya ce: “Shingen binciken Sojojin da aka kafa a Nasarawa, kusa da makabarta, ba ya aiki yadda ya kamata. Su ne ya kamata su tare ’yan bindigar, amma sun bar su suka wuce.
“Mun fi samun kwanciyar hankali lokacin da tsohon kwamandan Sojojin yake nan kafin a mayar da shi wani wuri. Hankalin kwamandan da ke yanzu yana kan mutanen da suke zuwa gona; ba sa barin mu mu je gonakinmu,” inji shi.
A wani labarin da ya shafi tsaro, wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sakkwato a yankin Kuka Mairahhu da ke ƙaramar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara.
ɗaya daga cikin matafiyan da lamarin ya rutsa da su ya ce an tilasta wa matafiya tsayawa, yayin da wasu daga cikinsu suka nemi mafaka a sansanin sojoji da ke Fangaltama.
Ya ce: “’Yan bindigar sun sanya mu a tsakiyar hanya, ta yadda suka tare gaba da baya, har da shingen sojojin. Dukkanmu mun makale,” inji shi.
Wata mata da ta tsira daga lamarin ita ma ta bayyana irin tashin hankalin da ta fuskanta, inda ta ce motarsu ta samu matsala a daidai lokacin da ’yan bindigar suka tare hanyar.
Ta ce: “Na shiga cikin matukar firgici lokacin da motarmu ta samu matsala, kuma ’yan bindigar suka tare hanya. Mutane sun makale kuma kowa ya rasa abin da zai yi.
“Bayan mun yi tunanin cewa an sake buɗe hanyar, motoci biyu da suka wuce gabanmu duk an yi garkuwa da mutanen da ke cikinsu. Mun samu ƙofofin motocin biyu a buɗe, amma ba mu ga kowa ba, ko kusa ko nesa,” inji ta.
Lamarin ya ƙara tayar da hankalin matafiya da mazauna yankin dangane da tsaron hanyar Gusau zuwa Sakkwato, wadda na daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗa Jihar Zamfara da makwabciyarta Jihar Sakkwato.
Haka kuma, hare-haren sun ƙara jawo hankali kan matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Zamfara, inda ’yan bindiga ke kai hare-hare kan al’ummomi da hanyoyi tare da yin garkuwa da matafiya.
Sai dai da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce har zuwa lokacin da aka tuntube shi bai samu rahoton waɗannan abubuwan ba.
Ya ce: “Ban samu wani rahoto kan hakan ba, amma zan tabbatar da bayanin sannan in dawo gare ku,” inji DSP Yazid.
A halin yanzu, babu wani cikakken bayani daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ko hukumomin soji da ya tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin hanyar Gusau-Sakkwato.
