Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yabawa jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da tsare-tsaren tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa sun kawo sakamako mai kyau da tasiri a fadin Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin Ministan Kudi da Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, tare da Ministan kula da Kiwon Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Dr. Muhammad Ali Pate, wadanda suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnati da ke Bauchi.
Yayin da yake miƙa goyon bayan jihar, Gwamna Mohammed ya bayyana cewa manufofin Gwamnatin Tarayya na yanzu suna samar da cigaba a aikace.
Ya tabbatar da cewa al’ummar Jihar Bauchi suna da masaniya kuma suna godiya ga kokarin gwamnatin wajen daidaita tattalin arziki da magance matsalolin tsaro, sannan ya yaba da kyakykyawar dangantakar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin jihohi.
Gwamnan Bauchin ya kuma jinjinawa shugaban ƙasa kan samar da ayyukan cigaba ba tare da la’akkari da bambancin siyasa ba inda ya bada misali da jihar sa ta Bauchi da kuma Oyo.
A ɓangaren samar da tsaro Gwamna Bala Mohammed ya jinjinawa yadda shugaban ƙasa ya aike da jami’an tsaro karkashin kulawar NSA da hukumomin soja wanda suka fatattaki ‘yan bindiga da suka addabi jihar a baya.
