Rundunar ‘yan sanda ta tsare sufeto da wasu biyu kan tatsar direbobi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Imo, Audu Bosso, ya umarci a kama tare da tsare wata sufeto da wasu jami’ai biyu na kare fararen hula na jihar ƙarƙashin Imo State Civil Guard Corps (IMSCGC) bisa zargin su da laifin tatsar masu ababen hawa. Kakakin rundunar, Henry Okoye a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya kuma umarci a gudanar da bincike akan al’amarin.

DSP Okoye ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis kuma jami’an sun yi iƙirarin cewa sun samu masu ababen hawan ne da laifin yin tuƙi ba tare da lasisi ba a Owerri, babban birnin jihar.

A shekarar 2013 ne aka kafa hukumar IMSCGC a Imo a lokacin mulkin Rochas Okorocha ƙarƙashin hukumar wayar da kan al’ummar jihar, kamar yadda a Kano ake da KAROTA.

An ga wani faifan bidiyo da nuna wasu jami’ai biyu sanye kakin IMSCGC da wata jami’ar ‘yan sanda suna neman a ba su cin hancin N35,000 daga wani direba bisa zargin cewa yana tuƙi babu lasisi, inda suka masa barazanar zai yi biya mai tsoka muddin ya bari suka kai shi ofis. Daga bisani sun yi jinga akan zai biya N15,000, inda a nan ɗaya daga cikinsu ya bayar da asusun banki kuma aka tura kuɗin a ciki.

Rundunar ‘yan sandan dai ta yi tir da wannan aiki, wanda ta ce ya ci karo da tsarin horo da mutuncin aikin hukumar musamman idan hakan ya faru da ɗaya daga cikin jami’anta.

Kakakin ya ce, a halin yanzu jami’an suna tsare kuma ana gudanar da bincike akansu, sannan za a ɗauki matakin doka akan dukkan wanda aka samu da hannu a laifin. Hukumar ta jaddada cewa babu wani aikin karya dokar tuƙi da ya halasta biyan cin hanci, cin mutunci ko saɓa wa ƙa’idar aiki.

By Babaji

Leave a Reply