2027: NDC za ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso ranar 20 ga Oktoba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta NDC ta sanar da shirinta na ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasa domin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyar ke cigaba da nazari kan bayar da manyan muƙamai.

Peter Obi, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambara ne, shi ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar tare da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin abokin tafiyarsa.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a Abuja ranar Asabar, Shugaban NDC na ƙasa, Cleopas Zuwoghe, ya ce jam’iyyar ta shirya tsarin kwamitin yaƙin neman zaɓen, amma tana yin shawara da Obi da Kwankwaso akan wasu muhimman muƙamai.

Zuwoghe ya bayyana cewa jam’iyyar tana ɗaukar lokaci nd wajen cimma matsaya akan naɗe-naɗen domin kauce wa zaɓo jami’an da biyayyarsu ga jam’iyyar ba za ta wadatar ba a yaƙin neman zaɓen.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa NDC ta buƙaci a gudanar da taron majalisar zartarwa (NEC) a ranar 20 ga Oktoba, inda a nan ne take fatan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen nata a hukumance rare da bayar da shaida ga ‘yan takararta. Ya ce, hakan zai ba ta dama wajen fara harkokin yaƙin neman zaɓen bisa yadda ya dace.

A watan Agusta ne dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayar da damar fara yaƙin neman zaɓen 2027 ga zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin ƙasa. Sannan a Satumba ne ta buɗe na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi.

By Babaji

Leave a Reply