Zargin badaƙalar kuɗi: Farfaganda da baƙin ciki ne – Shugabar NAWOJ ta Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida ta ƙasa (NAWOJ), reshen Jihar Nasarawa, Kwamared Mercy Tazan Zabadi, ta bayyana zargin da ake yi mata na karkatar da kuɗaɗe da kuma gudanar da ƙungiyar ita kaɗai a matsayin farfaganda da baƙin ciki.

Zabadi ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da jaridar Manhaja a Lafia, yayin da take mayar da martani kan zargin da wasu mambobin zartarwarta suka yi mata.

A cewarta, zargin ba shi da tushe balle makama kuma an yi shi ne da nufin ɓata mata suna da kuma na zartarwarta a idon ‘ya’yan ƙungiyar da jama’a baki ɗaya.

“A gaskiya, a fahimtata, farfaganda ce kawai da baƙin ciki a kaina, a kan exco ɗina da kuma Congress na NAWOJ Jihar Nasarawa baki ɗaya. Domin na san abin da na yi kuma zan iya bayar da hujja a ko ina, a kowane lokaci,” in ji ta.

Ta yi bayanin cewa dukkan kuɗaɗen da aka sakar mata, ciki har da na gwamnati, an yi amfani da su ne wajen abin da aka nufa da su, inda ta nuna cewa shirin da ake magana akai ba shirinta ne na ƙashin kanta ba, shiri ne na NAWOJ Nasarawa.

“Na san abin da na yi ta hannun exco ɗina, har ma da gwamnatin da ta saki kuɗin gare ni, abin da na faɗa musu shi ne abin da na yi. Dangane da shirin da na yi, dukkansu sun san cewa za mu gudanar da shiri, domin ba shirin Mercy Tazan ba ne, shiri ne na NAWOJ Nasarawa,” in ji ta.

Shugabar NAWOJ ɗin ta amince cewa saboda ƙarancin lokaci da kuɗaɗe, ta ɗauki alhakin ƙashin kanta domin ganin shirin ya yi nasara abin da ta ce wataƙila wasu mambobi suka fahimta ta wata fuskar.

“Duk da cewa a matsayina na shugaba, saboda ƙarancin lokaci da kuɗaɗe, na yi ƙoƙarin na ɗauki alhakin kaina domin ganin shirin ya yi nasara, ban san yin hakan zai zama matsala ba ko kuma zai ɓata wa wani rai ba. Amma duk farfagandar nan da baƙin ciki ba gaskiya ba ne,” ta ƙara da cewa.

Zabadi ta bayyana cewa an kafa kwamitoci a matakin jiha da na ƙasa domin bincikar lamarin, tana mai nuna ƙwarin gwiwa cewa gaskiya za ta fito fili.

“Godiya ga Allah an kafa kwamitin, na jiha da na ƙasa, za su duba dukkan abubuwan da ke ciki kuma za su fitar da rahoto kuma gaskiya za ta fito fili,” in ji ta.

Kan zargin da ake yi mata na gudanar da ƙungiyar ita kaɗai, shugabar ta musanta zargin, tana mai cewa a kullum tana tafiya da mambobin zartarwarta.

“Ba ni kaɗai ke tafiyar da kungiyar ba. Dalilin da ya sa suke cewa ni kaɗai ke tafiyar da ita shi ne saboda na aiwatar da wani ɓangare na shirin da kaina domin ganin ya yi nasara. Shi ya sa suke cewa ni kaɗai na yi. Dukansu suna cikin lamarin. Duk abin da na yi, ina sanar da su,” in ji ta.

Ta ce bayan shirin, ta gabatar da cikakken bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen ga exco, ta nemi afuwa inda ya kamata kuma ta yi tunanin an warware lamarin.

Kan tambayar ko tana da saɓani na ƙashin kai da sakatarenta wacce ke cikin masu yi mata zargin, Zabadi ta ce babu wata matsala ta ƙashin kai a tsakaninsu.

Da aka tambaye ta ko a shirye take ta miƙa kanta ga binciken kwamitocin da aka kafa, ta ce za ta jira sakamakon binciken.

“A yanzu ba zan iya cewa eh ba har sai an fitar da rahoto. Domin tunda ƙungiya ce, kuma tana gudanar da ayyukanta bisa ka’idoji da dokoki, muna bin hanyoyin da suka dace. An kafa kwamitin, tabbas za su bincika. Watakila idan na ce miliyan uku, wataƙila ba miliyan uku ba ne, miliyan shida ne, za su je su bincika su ga nawa aka sakar min da kuma yadda na kashe,” in ji ta.

Kan ko ta samu takardar dakatarwa a hukumance, Shugabar NAWOJ ta ce har yanzu ba ta samu ba.

“Har yanzu babu wanda ya bani takardar dakatarwa, har zuwa yanzu. Ko da safiyar yau shugabar ƙasa ta zo ta ce babu wanda ya bani takardar dakatarwa,” in ji ta, inda ta ƙara da cewa alhakin reshen jihar ne da ya yi zargin ya miƙa mata takardar dakatarwar.

By ukarofi

Leave a Reply