
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wajibi ne masu ababen hawa da ke fatan amfana da ragin Gwamnatin Tarayya na Naira 66 ga litar fetur su sauke manhajar Nigerian National Petroleum Company Limited ta wayoyin hannunsu wajen biyan kuɗin siyan fetur, yayin da sabon farashin bai kai ga samuwa ga kwastomomi a gidajen mai ba.
Wani bincike ya nuna cewa har zuwa ranar Juma’a a Abuja, ana cigaba da siyar da fetur akan N1,405 ga kwastomomi masu biya kai-tsaye a famfuna yayin da masu ababen hawa da ke amfani da manhajar suke saye akan N1,339.
Sakamakon binciken ya nuna cewa shirin gwamnatin na samar da sauƙin na da nufin rage raɗaɗin matsin tattali da al’umma ke ciki bisa tsadar fetur, musamman masu ababen hawa na ‘yan kasuwa, wanda a halin yanzu masu amfani da tsarin dijital ne kaɗai ke amfana da shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da NNPCL ya ƙara wa’adin ragin zuwa ranar 31 ga Oktoba, inda ake tsammanin kamfanin ya haƙura da jimillar ribar Naira biliyan 4.6 matuƙar cinikinsa na wata ya cancanci samun rangwamen.
Wakilin Manhaja ya gano cewa ana amfani da irin siyarwa guda a gidajen man na NNPCL a sassan babban birnin tarayyar.
Wannan al’amari dai ya haifar da tambayoyi musamman akan yadda sauran masu amfani ababen hawa da ba su da damar biya ta dijital za su amfana da rangwamen na wata guda.
