Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙaramin ministan tsaro Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya bayar da kyautar mota ɗaya da babura goma ga ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke goyon bayansa a Jihar Zamfara.
An bayar da tallafin ne ga ƙungiyar da Alhaji Salisu Dawa ke jagoranta a ƙarƙashin Matawalle Political Standing Committee (MPSC).
A cikin wata sanarwar ga manema labarai da sakataren yaɗa labarai na kwamitin, Yusuf Idris Gusau, ya fitar yau Asabar, Ministan ya ce wannan taimako wani ɓangare ne na shirinsa na ci gaba da ƙarfafa magoya bayansa masu yawa a jihar.
Matawalle, wanda Shugaban tafiyar siyasar sa a Jihar Zamfara, Injiniya Ibrahim Isa Mayana, ya wakilta, ya ce Matawalle zai ci gaba da tallafa wa mabiyansa a jihar.
A cewarsa, an bada tallafin ne domin sauƙaƙa wa waɗanda suka amfana,a matsayin godiya ga irin goyon baya da biyayya da suke nunawa ga tafiyar siyasar sa da kuma jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa waɗanda suka amfana za su yi amfani da ababen hawan domin amfanin kansu, iyalansu, da kuma jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa hakan zai sauƙaƙa yadda za a gudanar da ayyukan jam’iyya a faɗin jihar.
Matawalle ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa jajircewarsu wajen yaƙin neman zaɓen APC a dukkan sassan jihar da ma wajenta.
Da yake mayar da martani a madadin waɗanda suka amfana, shugaban ƙungiyar, Alhaji Salisu Dawa, ya nuna godiyarsa ga Ministan bisa wannan tallafi.
Ya bayyana cewa a baya, mambobin suna dogaro ne da wasu hanyoyin daban don isa ga al’ummomi daban-daban, amma da wannan tallafi, yanzu za su iya zagaya jihar baki ɗaya cikin sauƙi.
