Yadda ƙungiyar kawo cigaban ’Yan Arewa mazauna Ikorodu ta gudanar da taro a kasuwar Igbodu

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Kungiyar Arewa Development Association Ikorodu, wato ƙungiyar Kawo Cigaban ’Yan Arewa Mazauna ƙaramar Hukumar Ikorodu, ta gudanar da wani taro a yankin Igbodu Market da ke ƙaramar Hukumar Ikorodu a Jihar Legas.

An gudanar da taron ne a ranar Juma’a da ta gabata, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar, Mai Martaba Sarkin Hausawan Igbodu Market, Alhaji Bello Sale, domin ƙara haɗa kan mambobin ƙungiyar tare da neman shawarwarinsu kan hanyoyin tunkarar matsalolin da ka iya fuskantar al’ummar Arewa mazauna yankin.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar da mambobinta daga sassa daban-daban na ƙaramar Hukumar Ikorodu, da kuma ɗimbin Hausawa da sauran ’yan Arewa mazauna Igbodu Market da kewaye.

An gudanar da taron ne a harabar fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Igbodu Market, inda shugabannin ƙungiyar da sauran mahalarta suka gabatar da ra’ayoyi da shawarwari kan yadda za a ƙara bunƙasa ayyukan ƙungiyar.

Daga cikin shugabannin da suka halarci taron akwai Shugaban ƙungiyar, Alhaji Bello Sale; Mataimakinsa, Sha’aibu Lawan Igbodu; Sakataren ƙungiyar, Fasto Daniel Bala; Ma’ajin ƙungiyar, Alhaji Abbas Sunusi Igbodu; Uban ƙungiyar, Ahmed Sani Igbodu; da Babban Limamin ƙungiyar, Imam Malam Mustapha, da sauran shugabanni.

A yayin taron, Babban Limamin ƙungiyar, Imam Malam Mustapha, ya jagoranci addu’ar cika kwanaki uku da rasuwar Ali, wanda aka bayyana a matsayin ƙanin Sarkin Hausawan Igbodu Market, Alhaji Bello Sale.

Marigayin ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ta same shi a Legas, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida Gboza domin neman magani.

Mahalarta taron sun yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya kuma ba iyalansa da ’yan uwansa haƙurin jure rashin.

Bayan haka, mahalarta taron sun gabatar da jawabai daban-daban, inda suka bayyana ra’ayoyinsu da shawarwarin da suke ganin za su taimaka wajen ƙarfafa ƙungiyar da kuma samun ƙarin nasarori a nan gaba.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar Kawo Ci gaban ’Yan Arewa Mazauna Igbodu, Alhaji Bello Sale, ya bayyana farin cikinsa kan yadda jama’a suka fito da yawa domin halartar taron.

Ya ce babban dalilin kafa ƙungiyar shi ne taimakon juna da kare muradun ’yan Arewa mazauna yankin, musamman wajen tunkarar matsalolin da suke fuskanta da kuma samar da hanyoyin ci gabansu.

A cewarsa, mafi yawan mambobin ƙungiyar ’yan kasuwa ne, yayin da wasu ke gudanar da sana’ar haya da babura da sauran sana’o’in dogaro da kai.

Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta wajen kare mutunci da muradun ’yan kasuwa, tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu da harkokin kasuwancinsu.

A ƙarshe, Alhaji Bello Sale ya taya Nijeriya murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da yi wa ƙasar addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya kuma yi fatan Allah Ya ci gaba da zaunar da al’ummar Nijeriya lafiya tare da ƙara tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin ’yan ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply