Mambayya sai mai nazari

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Malam Aminu Kano bai gina gidansa “Mambayya” a 1968 don taron ranar zallawa ba. Wallahi ko sunan gidan ba su iya rubutawa daidai ba! maimakon Mam-bayya sai su ka maka Man-bayya. ƙarshe na ga Zallawa sun bayyana inda za su yi taron ranarsu ta zallanci da fakewa da wai ranar Hausa a gidan MAMBAYYA inda su ka rubuta MANBAYYA da “N” maimakon “M” don dama ’yan arufta ne ba sa iya rubutu ko magana da Hausa tiryan-tiryan sai sun wurga Turanci. Hausa ba layinsu ba ne sam.

MAMBAYYA gidan marigayi Malam Aminu Kano ne da ya gina a 1968 don jama’arsa ta NEPU inda a 1989 gwamnatin mulkin soja ta karɓi gidan ta kafa cibiyar nazarin harkokin dimokuraɗiyya. A 1999 gwamnati ta miƙa gidan ga jami’ar Bayero wacce ita kuma a shekara ta 2000 ta maida shi cibiyar nazarin dimokuraɗiyya ta Malam Aminu Kano. Sunan MAM-BAYYA laƙabin mahaifiyar Malam Aminu ne wato MATAR WAMBAI.

Wasu daga Zallawa sun taba yi wa Malam Aminu sharri wai Sardauna ne ya turo shi ya zama ɗan adawa don amfani da shi don gallazawa Hausawa! Wasu ma sun ce wai Malam ɗin Bafulatani ne don haka ba zai yi wa Hausawa adalci ba. Duk dai irin logar makirci na ‘yan bazata da ke barandar AIFOB wajen aikin wargaza Arewa don cimma buri ta bulus a kafa ƙasar aware ta Biyafara da kuma maida yankin ƙirƙira Midil Bel ya zama ba Arewa ba.

Hakika ba a tanadi gidan MAMBAYYA don rawa da waƙa ko damben gargajiya ba balle har wasu masu hula hana-sallah da ko sunan gidan ba su iya rubutawa ba su shigo wai za su yi taro da sunan Hausa! Kai akwai mamaki haka ya faru a Kano tsakanin duk masu ilimi da kuma nazarin harshen Hausa da al’adun Hausawa. Waɗannan mutane dai ba su cancanci amfani da sunan Hausa sukutum wai za su yi taro na ranarsa ba.

Na sha shaida mu ku ba wata kungiya sam-sam mai suna “Hausawan Nigeria” sai “Gidauniyar Hausawa” kamar yadda su kansu Zallawan su ka rubuta da kansu. Zai zama karya doka su nemi hurumin taro a MAMBAYYA da sunan ƙungiya sai dai Gidauniya.

Shin wa zai ba da tabbacin makiya Shehu Mujaddadi ba za su nemi shiga gidan Mambayya ba. Yaya za a yi hukumar wannan gida ko jami’ar Bayero za su bar irin waɗannan mutane masu wannan manufa su yi taro a gida mai daraja da ke ɗauke da sunan Malam Aminu?

Duk wanda ya halarci taron zallawa da sunan ranar hausa to haƙiƙa ya cancanci a ja ma sa kunne ko ladabtarwa. Ina kira ga gwamnatin Kano ta takawa Zallawa birki don cin mutuncin Hausawan ya isa hakanan

Ni na ma wuce batun ranar Zallawa da bagayen wai ranar Hausa, sai na ga har yanzu wasu na zakewa ko da gangan ko jahilci kan fahimtar wannan taro fakewa ne da guzuma don a harbi karsana. Duk masu hayaniyar nan a soshiyal midiya ba su da alaka da Hausa sai zangar wannan muguwar kwangilar wargaza Arewa ta sanya rigar karya ta Hausa wato logar ƙura da fatar akuya.

Wai asalin taron shi ne wasu Zallallu sun yi taro ko a Tiktok ko wata kafar soshiyal midiya sai su ka ga me zai hana su juya wannan zuwa taron ranar Hausa! Ka ji sai ka ce a Tiktok a ka ƙirƙiri Hausa. Don rashin kunya a rasa ma inda za a yi wannan magana sai a tsirara a yanar gizo. Duk da ma ba mamaki don masu shirya abun yawanci ’yan ƙananan yara ne da ba su san ma inda duniya ta dosa ba, duk inda guguwa ta kada sai su garzaya can kamar taron ledoji a juji idan guguwa ta kada sai ta watsa su kan jinka da salga ba zabi.

Ina nanatawa cewa masoya manyan harsuna kan yi taruka ne kan ADABI na harshe kamar ranar Turanci inda a ke yi don girmama Shehun Shehunai na adabin Turanci wato William Shakespeare SHEHU GIRGIZA MASHI. Duk wanda ya karanta ADABI na Turanci ya san waye Shehu Gizgiza Mashi 1564-1616. A kan yi hakan ranar 23 ga Afrilu. Ranar Larabci ma 18 ga Disamba don ADABI da duba ayyukan Gangaran a harshen ka fi Gwani SIBAWAIHI. Majalisar ɗinkin Duniya ta dau Larabci a matsayin ɗaya daga harsuna 6 da a ke amfani da su a tarukan majalisar a 1973 kuma an yi hakan 18 ga Disamba.

Duk irin waɗannan taruka ba rawa ba waka ba dambe ba ƙabilanci ba AIFOB da Midil bel; a kan duba tsantsar ilimin ADABI ne don masu ilimin harshe ke taron kuma ba lallai ma ‘yan harshen ba. Shi ya sa a kiyayi abun da tantiran jahilai da ‘yan arufta su ka tsara don cimma burin makiya Lardin Arewa.

Ina kira ga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su dau matakan dakatar da duk wani Bazalle daga yin irin wannan taro don akwai ɓoyayyiyar manufa fiye da abun da a ke yayatawa na fili. A takawa Zallawa birki don wani lokacin mai karambani sai an zungure ma sa hanci ya san akwai hukuma a kasa.

Gabanin gudanar da wannan taro da ba shi da tushe, Zallawa sun shirga karya wai sun yi taro da Sarkin Hausawan Keffi Alhaji Uwaisu Danbawa. Mai martaba Sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa bai nada Alhaji Danbawa don Zallawa ba sam-sam.

Na ga Zallawa na yayata hotunan wasu matasa da Sarkin Hausawan Keffi a jihar Nasarawa Alhaji Uwaisu Danbawa da nuna sun yi taro ne da Sarkin Hausawan kuma tamkar karfafa tafiyar zallanci ne. Wannan labari sam ba haka ba ne don matasan nan dai sun je ne taya murna ga Alhaji Danbawa wanda mai martaba Sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa ya daukaka darajarsa daga KACHALLAN KEFFI zuwa SARKIN HAUSAWA. Wallahi dududu daga naɗin Alhaji Danbawa zuwa yau da na ke rubutun nan kwana 21 ne kacal!.

Masu taya murna da sauran masoya bayan naɗin a ranar 31 ga watan jiya Yuli 2026 na da damar zuwa taya murna kamar yadda a ke yi idan wani ya samu irin wannan mukami. Kuma nadin don kara karfafa hadin kai da zaman lafiya ne a Keffi ba wai don kawo tsagerancin Zallawa ba. Kamar yadda mu ka taya murna ga abokinmu Sarkin Hausawan Nyanya a Abuja Alhaji Musa Dala, hakanan Insha Allah za mu shiga Keffi don yin murna ga Alhaji Uwaisu. Zallawa tamkar kaska ne rabi mai jini ba su da alaka da Hausawa sai kan kwangilarsu ta wargaza Arewa da yaƙi da Musulunci da cin zarafin Hausawa ta ƙarƙashin kasa.

Abun da bai yi min daɗi ba shi ne yadda matasan nan da su ka gana da Alhaji Uwaisu Danbawa ba su yi shiga irin ta Hausawa ba. Hakika ya kamata ko a Turai ne har dai Hausawa za su yi ziyara don lamarin da ya shafi harshensu ko al’ummarsu, a ga sun saka sutura irin ta gargajiyar Hausawa aƙalla dai doguwar riga da hula ko da ba rawani. Akwai ma wanda na hango a hoton ziyarar kamar da askin shalama na ‘yan gayu a kansa. Akasarin su ba hula a kansu sai kamar mutum daya da kuma wani da ya wurga kwallan kansa cikin hula hana-sallah! Ai da mamaki a ce Bahaushe zai ziyarci Sarkinsa amma ya wurga kansa cikin hula hana-sallah. Hakan na nuna rashin da’a ko rashin sanin ya-kamata.

Tabbas zan jagoranci shaidawa mai martaba Sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa labarin bullar wasu ‘yan barandar AIFOB a yanar gizo da ke neman haddasa mummunar fitina tsakanin al’ummar Musulmi dama zagin Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo. Mai girma Kachallan Keffi wanda yanzu ya zama Sakin Husawa zai yi aiki ne na kawo zaman lafiya a masarautar Keffi don haka ba alamun zai yi maraba da Zallawa masu shigar burtu waɗanda ko Hausar ba ta yiwuwa a bakinsu sai sun wurga Turanci nan da can. Duk yankuna irin Gidan Zakara, Uke, Tudun Wada da duk matsugunan da ke kewaye da Keffi ba za su kyale Zallawa su shafa mu su bakar aniya ba. Mazauna wadannan yankuna na da mabiya addinai da kabilu daban-daban kuma babban abun muradi shi ne zaman lafiya ta hanyar mutunta juna. Masu noma su yi noma masu kiwo su yi kiwo don kasa ce mai yalwar yabanya da ma albarkatun ƙasa da dama.

KAMMALAWA

Kamar sauran masarautun Arewa masu tarihi daga tajdidin Shehu Mujaddadi, masarautar Keffi wacce Malam Abdu Zanga ya assasa a 1802 na daga yankunan da ke bin kiran Shehu Mujaddadi. Keffi a baya na karkashin masarutar Zazzau ne wacce Malam Musa ya ƙarfafa tafiyar addini a cikinta. Har gobe mai martaba Sarkin Keffi na zama wakilin Sarkin Musulmi a ayyuka da dama na addini da zaman lafiya. Don haka ba ta yadda Alhaji Uwaisu Danbawa zai haɗa kai da makiya musulunci ko kulle-kulle na neman haddasa fitinar ƙabilanci da ka iya kawo koma baya a yankin da al’umma su ka cakuɗe ta zamantakewa tsawon shekaru aru-aru kuma baki ma daga wasu sassan kasa su ka shigo a ke zaune lami lafiya.

Na tabbata dattawa, hukumomin tsaro da duk masu ƙaunar Arewa na yin duk abu mai yiwuwa na ɗorewar tasirin wannan Lardi kamar yadda iyaye da kakanni su ka ƙarfafa yankin da addu’a da tarbiyya.

By ukarofi

Leave a Reply