Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon tallafin abinci, kuɗaɗe da sauran kayan agaji ga al’ummar ƙaramar hukumar Musawa da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa.
Tallafin ya samu ne da haɗin gwiwar da ɗan majalissar tarayya mai wakiltar yankin Hon. Abdullahi Aliyu (Dujiman Katsina), sun haɗa kai domin tallafa wa al’ummar yankin tare da rage musu raɗaɗin halin da suke ciki.
An raba buhunan shinkafa 1,500 da buhunan taki 200, yayin da Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad (Dujiman Katsina), Ɗan Majalissar Tarayya mai wakiltar yankin, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 domin tallafa wa al’ummomin da lamarin tsaro ya shafa, ya kuma bada babura 109.
Sauran wanda suka bada gudunmuwar akwai Muhammad Abu Ibrahim da ministar al’adu, fasaha da tattalin arziki, Hon. Hannatu Musa Musawa ta bada naira miliyan 10.
Da yake jawabi, Gwamna Raɗɗa ya yaba da wannan kyakkyawan yunƙuri na ƴaƴan Musawa da Matazu, yana mai bayyana tallafin a matsayin wata muhimmiyar gudunmawa wajen rage wa al’ummar da suka fuskanci hare-haren ta’addanci raɗaɗin halin da suke ciki.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati, shugabannin siyasa da al’umma wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da sauran matsalolin da ke fuskantar jama’a.
