Macen Afirka ba ta jiran sai an ba ta — Funmilayo Ransome-Kuti
Daga AISHA ASAS
Akwai wasu mata da tarihinsu yake sa ka tsaya ka tambayi kanka irin duniyar da suka rayu a cikinta. Domin abubuwan da suka yi a yau za su iya zama kamar abubuwan da kowa zai iya yi, amma idan aka mayar da kai shekaru ɗari baya, sai ka fahimci cewa abin da suka yi ba ƙaramin ƙalubale ba ne. A lokacin da mace ke da ƙarancin damar yin karatu, balle ta shiga harkokin siyasa ko ta tsaya a gaban dubban mutane tana neman a saurare ta, akwai wadda ta riga ta fahimci cewa shiru ba zai kawo canji ba.
Wannan ita ce Funmilayo Ransome-Kuti.
Ta kasance malama, mai fafutukar ‘yancin mata, ‘yar kishin ƙasa kuma ɗaya daga cikin fitattun mata da suka taka rawa a tarihin siyasar Najeriya kafin da bayan samun ‘yancin kai. Amma idan aka takaita tarihinta da waɗannan muƙamai da siffofi, za a rasa ainihin abin da ya sa ta cancanci a kira ta Gimbiya. Domin babban abin da ta yi bai tsaya ga neman abin da zai amfani kanta ba; ta yi amfani da iliminta da matsayinta wajen tara mata, koya musu yadda za su fahimci hakkokinsu, sannan ta kai muryarsu inda ba za su iya kaiwa su kaɗai ba.
Shin wace ce Funmilayo Ransome-Kuti?
An haifi Funmilayo a Abeokuta a shekarar 1900, a lokacin da Najeriya ke ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya. An haife ta cikin gidan da ya fahimci muhimmancin ilimi, kuma wannan ya taimaka wajen buɗe mata wata hanya da ba ta saba buɗewa ga ‘yan mata da yawa a wancan lokaci ba. Ta zama mace ta farko da ta shiga Abeokuta Grammar School a matsayin ɗaliba, kafin daga baya ta tafi Ingila domin ci gaba da karatu. Bayan ta dawo Najeriya a shekarar 1922, ta koma makarantar da ta yi karatu a cikinta, inda ta fara koyarwa.
Saidai ilimi a wurinta bai kasance takardar shaidar da za ta rataya a bango ba. A hankali ya zama hanyar da ta fahimci yadda za ta taimaka wa wasu. Ta fara koyar da mata karatu, musamman matan da ba su samu damar zuwa makaranta ba.
A shekarar 1944 ta kafa Abeokuta Ladies Club, wadda a farkonta ta ƙunshi mata masu ilimi, malamai da wasu masu sana’o’i. Da farko ayyukanta sun fi karkata ga jinƙai da taimakon juna, amma hakan ya sauya ne bayan mata daga kasuwa suka fara zuwa wurinta suna neman a koya musu karatu da ɗinki.
A nan ne wani abu mai muhimmanci ya faru a rayuwarta. Ta fara ganin cewa matsalolin mata ba matsalolin mutum ɗaya ba ne. Matar kasuwa da ta zo neman karatu ba wai kawai tana fama da rashin sanin rubutu ba ne; tana cikin tsarin da ke iya tauye mata kuɗinta, ‘yancinta da damar da take da ita ta bayyana ra’ayinta. Ta haka ne aikin koyarwa ya fara sauya mata fahimtar abin da ya kamata ta yi.
A yayin da take ƙara kusantar matan kasuwa, ta fahimci irin matsin da suke ciki sakamakon dokokin mulkin mallaka, musamman tsarin sarrafa farashi da haraji. Akwai lokutan da aka tilasta wa mata sayar da kayan abinci kamar shinkafa da garri a farashin da gwamnati ta kayyade, kuma wasu jami’ai sukan kwace kayan ba tare da biyan kuɗi ba. Wannan ya sa ƙungiyar da ta kafa ta fara barin aikin jinƙai kawai, ta koma ƙungiyar da ke neman a gyara tushen matsalar.
A shekarar 1946 aka sauya sunan ƙungiyar zuwa Abeokuta Women’s Union, wadda Funmilayo ta zama shugabarta. Abin da ya sa wannan ƙungiya ta zama daban shi ne haɗuwar mata masu ilimi da matan kasuwa. Wannan haɗin ya ba mata damar haɗa ƙarfi a kan matsalolin da suka shafe su baki ɗaya, maimakon kowace ƙungiya ta yi gwagwarmaya ita kaɗai. A wasu bayanan tarihi, ƙungiyar ta samu kusan mambobi 20,000, yayin da mata masu yawa a Abeokuta suka nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar.
Ko me ya sa ta canza akalar tafiyar ƙungiyar tata?
Abin da ya fara da koyar da mata karatu ya koma gwagwarmayar siyasa ne lokacin da Funmilayo ta fahimci cewa ba za a iya taimaka wa mata da koyar da su karatu kawai ba idan tsarin da suke rayuwa a cikinsa yana ci gaba da tauye musu haƙƙi.
A Abeokuta, haraji ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka haɗa mata wuri guda. Mata na fuskantar tsarin haraji da suke ganin ba na adalci ba ne, yayin da ba su da wakilci a tsarin mulkin da ke karɓar kuɗin daga gare su. A takaice dai, ana son su biya, amma ba a ba su damar cewa komai game da yadda ake mulkarsu ba.
Funmilayo da matan Abeokuta Women’s Union suka fara amfani da hanyoyi daban-daban wajen neman a saurare su. Sun rubuta koke-koke, suka aika saƙonni, suka shirya taruka, suka gudanar da zanga-zanga, sannan suka yi amfani da haɗin kan mata wajen matsawa hukumomi lamba. Lokacin da aka fara hana su yin zanga-zanga a fili, ba su daina ba; sai suka sauya dabaru. Sun shirya abin da za a kira taron sada zumunta ko biki, amma a zahiri matan sun taru ne domin ci gaba da bayyana matsalolinsu.
A wasu daga cikin zanga-zangar, dubban mata sun fito. Wannan ba ƙaramin abu ba ne a wancan lokaci, domin ba wai kawai mata suna fitowa ne suna magana da hukumomi ba; suna ƙalubalantar tsarin mulkin da ya saba ganin su a matsayin waɗanda za su zauna su saurara.
Gwagwarmayar ta ƙara tsananta, har ta kai ga cewa a shekarun 1947 da 1948, Funmilayo da sauran shugabannin ƙungiyar suka fuskanci tsangwama daga hukumomi da masu mulki. Matan sun ci gaba da matsa lamba, yayin da hukumomi suka yi ƙoƙarin hana tarukansu da zanga-zangarsu. Daga ƙarshe, wannan gwagwarmaya ta taimaka wajen kawo sauye-sauye masu muhimmanci a tsarin harajin mata da kuma tsarin mulkin gargajiya na Abeokuta.
Wani abin da ya fi ban sha’awa shi ne cewa Funmilayo ba ta tsaya tana magana a madadin mata kawai ba. Ta koya musu yadda za su yi magana da kansu. Ta haɗa mata masu karamin ƙarfi da masu ilimi, ta sa suka fahimci cewa matsalolin da suke fuskanta ba dole ne su ɗauke su a matsayin ƙaddarar rayuwa ba. Wannan shi ne babban abin da ya sa tasirinta ya wuce zanga-zangar haraji.
ƙalubalen da Funmilayo Ransome-Kuti ta fuskanta:
Rayuwar Funmilayo ta ƙunshi ƙalubale iri-iri, kuma wasu daga cikinsu sun fito ne kai tsaye daga tsarin mulkin mallaka da ta yi adawa da shi, yayin da wasu suka taso daga tunanin al’umma game da abin da mace ya kamata ta yi. Ta shiga fagen da ba a saba ganin mata a cikinsa ba, kuma duk lokacin da ta ɗaga murya kan abin da ta ɗauka a matsayin rashin adalci, tana fuskantar masu ganin cewa bai kamata mace ta kasance a wannan wuri ba.
A gwagwarmayar Abeokuta, matan da take jagoranta sun fuskanci barazana, kama da tsangwama. Hukumomi sun yi ƙoƙarin hana zanga-zangar, yayin da wasu jami’ai suka yi amfani da ƙarfin gwamnati wajen raunana masu fafutuka. Amma Funmilayo ta fahimci cewa idan ƙungiyar mata ta tarwatse saboda tsoro, to za a mayar da su inda suka fito. Saboda haka ta yi ƙoƙarin ƙarfafa mata su tsaya tare, har ma ƙungiyar ta tanadi taimakon doka ga mambobin da aka kama.
Wani ƙalubalen kuma shi ne yadda gwagwarmayar siyasa ta shafi rayuwarta ta sirri. Mijinta, Reverend Israel Ransome-Kuti, ya kasance mai goyon bayanta kuma auren nasu ya kasance na fahimtar juna, rasuwarsa a shekarar 1955 ta kasance babban rashi. Duk da haka, ba ta bar wannan rashi ya sa ta yi ritaya daga aikin jama’a ba. Ta ci gaba da gwagwarmaya a fagen siyasa da na ƙungiyoyin mata.
A siyasar jam’iyya ma ta fuskanci ƙalubale. Ta kasance cikin masu kafa da shugabanci a National Council of Nigeria and the Cameroons, amma lokacin da ta nemi takarar kujerar Majalisar Wakilai a shekarar 1959, jam’iyyar ta ƙi tsayar da ita a matsayin ‘yar takararta. Ta yanke shawarar tsayawa a matsayin ‘yar takara mai zaman kanta, amma rabuwar masu goyon bayanta ta sa ita da ɗan takarar jam’iyyar suka kasa samun nasara. Daga baya ta kafa Commoners’ People’s Party, amma jam’iyyar ba ta daɗe ba.
Wannan wani ɓangare ne na tarihin da ke nuna cewa ko da mace ta sami suna da karɓuwa, shiga tsarin siyasa na ƙasa ba ya zama abu mai sauƙi. Funmilayo ta iya tara dubban mata a Abeokuta, amma ikon da ƙungiyar mata ta ba ta a matakin gida bai sauya kai tsaye zuwa ikon jam’iyya da zaɓe a matakin ƙasa ba.
A shekarun baya, matsalolinta suka ƙara shafar alaƙarta da hukumomin Najeriya da na ƙasashen waje. Saboda ra’ayoyinta na kishin ƙasa, adawa da mulkin mallaka da kuma alaƙarta da ƙungiyoyin mata na duniya, hukumomi sun taɓa kallonta da shakku tare da zargin kusancinta da akidar kwaminisanci. A shekarar 1957 gwamnati ta ƙi sabunta fasfo ɗinta, sannan a shekarar 1958 aka hana ta bizar shiga Amurka domin halartar wani taron ƙungiyar mata.
Nasarorin da Funmilayo Ransome-Kuti ta samu:
Idan aka ce Funmilayo ta yi nasara ne kawai saboda ta jagoranci zanga-zangar Abeokuta, za a rage girman abin da ta bari. Babbar nasararta ita ce ta taimaka wajen canza yadda ake kallon mace a cikin harkokin jama’a. Ta nuna cewa mace ba dole ta tsaya a bayan gida tana jiran a yanke hukunci a kanta ba; za ta iya fahimtar abin da ke faruwa a al’umma, ta shirya jama’a, ta yi magana da hukumomi, ta shiga siyasa kuma ta nemi a saurari muryarta.
Abeokuta Women’s Union ta zama ɗaya daga cikin manyan misalan yadda mata za su iya haɗa kai su matsa lamba kan gwamnati. Gwagwarmayar ta taimaka wajen kawo ƙarshen wani tsarin haraji da mata suka ɗauka a matsayin rashin adalci, sannan ta taimaka wajen kawo sauyi ga tsarin Sole Native Authority na Abeokuta. A wasu bayanan tarihi, Alake Ademola ya yi murabus daga sarauta a sakamakon rikicin da ya taso tsakanin hukumomi da ƙungiyar mata, kafin daga baya ya dawo.
Funmilayo ta kuma taka rawa wajen faɗaɗa gwagwarmayar mata daga Abeokuta zuwa matakin ƙasa. A shekarar 1953 ta shirya taron mata a Abeokuta wanda ya samu halartar wakilai kusan 400, daga baya aka kafa Federation of Nigerian Women’s Societies, wadda ta yi fafutukar neman ‘yancin zaɓe ga mata, ƙarin damar ilimi da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya da jinƙai.
Za muci gaba.
