Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Da safiyar ranar Lahadin nan gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da rasuwar Alhaji Garba Muhammed Kola da aka fi sani da Kanga.
Alhaji Garba Muhammed Kola ya rasu a garin Birnin Kebbi bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwar da shi ne shugaban sashen tsare-tsaren wasannin al’adun gargajiya a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kebbi.
Ya rasu ya bar mata uku da yaya da dama.
An kuma yi jana’izar sa a garin Birnin Kebbi kamar yadda shari’ar musulunci ta tanada.
Kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi da babban Sakatare Alhaji Alkasim Salihu Gunabi da daraktoci daga wannan ma’aikatar sun halarci jana’izar.
Babban Sakatare Alhaji Alkasim Salihu Gunabi ya bayyana rashin Kola ba ƙaramin giɓi ya bari ba a fagen isar da saƙonni ga al’umma ba.
Ya ce ba shakka an rasa ma’aikacin da za a daɗe ana tunawa saboda ƙwazon sa da kuma sadaukar da rayuwar sa wajen fito da jihar Kebbi a idon duniya wanda ya jagoranci ‘yan wasan gargajiyar jihar ciki da wajen ƙasar nan inda aka samo lambobin yabo da dama.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan sa ya bai wa ‘yan uwa da masoya haƙurin jure wannan rashin.
