Shahararren jarumin Nollywood, Taiwo Hassan Ogogo ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen jarumin Masana’antar Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo ya rasu. ‘Yarsa Kira Taiwo ce ta tabbatar da rasuwarsa a wani faifan bidiyo da aka yi kai-tsaye yayin tattaunawa a shafinta na Instagram.

A ranar Litinin, 17 ga Agusta ne ‘ya’yan Ogogo biyu, wato Kira Taiwo da Lima Taiwo suka fitar da wani faifan bidiyo, inda suke roƙon jama’a shawarwarin lafiya da agaji ga mahaifin nasu da ya kasance yana fama da cutar daji ta mataki na huɗu.

A cewar Kira, likitoci sun ce ba za su yi masa aikin kashe ƙwayoyin hallitar da ke girma da wuri ba (chemotherapy) saboda halin da yake ciki. Akan haka ne, iyalan nasa suka fara neman mafita ciki har da wasu nau’ukan magani na musamman da na gargajiya.

Ta bayyana cewa, iyalan ba sa neman taimakon kuɗi, saidai suna buƙatar shawarar magani da za ta taimaka wa mahaifin nasu wajen warkewa daga cutar. Sannan, ta kuma ce wasu asibitoci da dama sun ƙi karɓar sa saboda matakin cutar, lamarin da ya sa suka shiga fargabar rasa shi.

Kira ta tabbatar da rasuwarsa mahaifin nasu Ogogo ne a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, wanda ya rasu yana da shekara 66 a duniya.

By Babaji

Leave a Reply