
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya koma Jam’iyyar APC a hukumance gabanin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Hakan na zuwa ne bayan shawarwari da abokan hulɗar siyasa da kuma tattaunawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Bindow ya sake rajistar zama mamban jam’iyyar ne a mazaɓarsa da ke Mubi, wato cibiyar kasuwanci ta jihar Adamawa a ranar Lahadi, a gaban Shugaban APC na mazaɓar, Alhaji Ahmadu Guruja.
A yayin haka ne aka samu halartar tsofaffin magoya bayansa, abokai, ‘yan dangi, abokan harkokin siyasa da masu fatan alheri, waɗanda suka taru don masa maraba da dawowa cikin jam’iyyar mai mulki.
Da yake jawabi a wajen taron, Bindow ya ce ya jima yana girmama ɗa’ar da ke cikin APC musamman wajen ƙaurace wa ayyukan da za a kira da zagon-ƙasa ga jam’iyyar, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne saboda dacewar jam’iyyar ga tsare-tsaren siyasarsa na tsawon lokaci da kuma shawarwari da abokan siyasa da kuma Sanata Shettima, wanda ya ɗauka a matsayin ɗan uwa kuma amini.
