Magidanci ya zuba wa matarsa fetur ya banka mata wuta saboda riga

Spread the love

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kogi ta kama wani mutum mai shekaru 33, Jacob Irewa, bisa zargin banka wa matarsa wuta a lokacin da suka samu saɓani a gidansu.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 14 ga Agusta, a Oworo Estate da ke Felele, Lokoja, babban birnin jihar Kogi, kamar yadda Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Afusat Saliu, ta bayyana.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Lokoja, Saliu ta ce matar, mai suna Berida Irawo, ta samu raunuka kuma ana duba lafiyarta a Asibitin Honey Gold da ke Felele.

Ta ce, jami’an Sashen B na Rundunar ’Yan Sanda, ƙungiyar sa ido ta Felele, sun isa wurin bayan samun rahoton gaggawa, inda suka kama wanda ake zargin a wurin da lamarin ya faru.

Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna cewa saɓanin ya samo asali ne bayan matar ta ƙona wasu daga cikin tufafin mijinta ba tare da izininsa ba.

Sai dai rikicin ya ƙara tsananta, inda ake zargin Irewa ya yi wa matarsa barazana, sannan ya tsotse fetur daga babur ɗinsa, kafin daga bisani ya zuba mata tare da ƙoƙarin cinna mata wuta.

A cewar kakakin rundunar, wanda ake zargin ya amince a bayaninsa ga ’yan sanda cewa shi ne ya banka wa matarsa wuta.

Rundunar ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike domin gano cikakkun bayanan abin da ya faru da kuma tattara ƙarin hujjoji.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, CP Naziru Kankarofi, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin abin tashin hankali da ba za a amince da shi ba.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali ba, musamman a cikin gidaje, tare da kira ga al’umma da su riƙa warware rikice-rikice ta hanyoyin doka.

Kankarofi ya ce, rundunar ba za ta amince da duk wani mataki da ka iya jefa rayuwar mutane cikin haɗari ba, yana kuma ƙarfafa jama’a da su nemi hanyoyin lumana da na doka wajen sasanta duk wata taƙaddama.

Rundunar ta ce, za a gurfanar da Irewa gaban kotu bisa zargin yunƙurin kisan kai bayan kammala bincike.

Haka kuma, rundunar ta tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu tare da tabbatar da cewa masu aikata laifukan tashin hankali sun fuskanci hukunci.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani lamari na cin zarafi a cikin gida da wuri, domin a daƙile shi tun kafin ya rikiɗe zuwa mummunan tashin hankali.

By ukarofi

Leave a Reply