Auren Adam Zango na takwas ya ƙara tayar da ƙura 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure a Jamhuriyar Nijar, kwanaki kaɗan bayan kawo ƙarshen aurensa da jaruma Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty.

Rahotanni sun ce an ɗaura sabon auren ne a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, da wata ’yar ƙasar Jamhuriyar Nijar. Zango ya tabbatar da sabon auren ta hanyar wallafa hotonsa tare da sabuwar amaryarsa, inda ya bayyana farin cikinsa da wannan sabon babi na rayuwarsa.

A cikin saƙon da ya wallafa bayan auren, jarumin ya nemi masoyansa da su ci gaba da yi masa addu’ar samun zaman lafiya da ɗorewar sabon auren. Ya kuma bayyana cewa ya shiga wannan aure ne da fatan samun dacewa, yana mai cewa bai taɓa yin aure da niyyar rabuwa da matar ba, abin da ya faru a baya kuwa ya danganta shi da ƙaddara.

Sabon auren ya zo ne bayan ɗan gajeren lokaci da Adam A. Zango ya rabu da Maimuna Pretty, wadda ya aura a watan Agusta 2025. Rahotannin rabuwar sun fara yaɗuwa ne a ƙarshen watan Yuli, kafin Zango ya fito a ranar a 1 ga Agusta 2026 ya tabbatar da cewa auren ya mutu.

Da yake magana kan rabuwar, Zango ya ce shi da Maimuna sun gano cewa dukansu suna da genotype iri ɗaya wato AS, kuma wannan na daga cikin dalilan da suka kai ga kawo ƙarshen auren.

Jarumin ya ce ya fito ya bayyana hakan ne domin ya sanar da masoyansa gaskiyar abin da ya faru, maimakon a bar jita-jita da bayanan da ba su da tushe su ci gaba da yaɗuwa. Ya kuma roƙi jama’a da su mutunta sirrin lamarin da mutuncin ɓangarorin biyu.

Zango ya kuma wallafa wani bidiyo da ya ce an ɗauke shi a ranar da Maimuna ta tattara kayanta ta bar gidansa. A cewarsa, rabuwar ta gudana cikin kwanciyar hankali da mutuntawa, ba tare da wani rikici ba. 

Sabon auren ya sake jawo cece-ku-ce a tsakanin masu bibiyar Kannywood, musamman saboda yadda ya zo cikin can gajeren lokaci bayan rabuwar aurensa da Maimuna. Wasu sun taya jarumin murna tare da yi masa addu’ar zaman lafiya, yayin da wasu suka sake buɗe batun yawan aure da saki da ya yawaita a rayuwar jarumin.

By ukarofi

Leave a Reply