Ronaldo ya bayyana cikakken labarin dalilin barinsa tawagar Portugal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zakaran ɗan ƙwallon ƙafa na duniya Cristiano Ronaldo, ya fitar da wata sanarwa da a ciki yake zargin kociyan Portugal, Jorge Jesus da cin amana a lokuta mabambanta, inda ya bayyana hakan a matsayin rikicin da ya sabbaba masa barin tawagar ‘yan wasan ƙasar.

Kyaftin ɗin tawagar mai shekaru 41 ya bayyana cewa, da fari ya ƙudiri aniyar yin ritaya bayan kammala gasar Kofin Duniya na 2026, amma daga bisani shugaban hukumar ƙwallon ƙafan Portugal ya shawarce shi da ya cigaba da wakiltar ƙasar kuma ya amince da hakan.

Da farko, Ronaldo ya goyi bayan naɗin Jesus a matsayin mai horar da ‘yan tawagar amma daga bayan an fara samun tsamin danganta yayin da ake buga wasannin ƙasa-da-ƙasa kan gudanarwar harkokin wasanni, ciki har da bai wa ɗan wasan isasshen lokacin buga wasa.

Ainihin abin da ya haifar da rashin jituwarsa da kocin shi ne tsara yanayin atisaye daga lokacin gabanin fara kakar wasa, wanda da fari ya nuna cewa Ronaldo zai kasance ba tare da tawagar ba yayin da za ta kara da Norway da Denmark domin kula da lafiyarsa. Saidai ɗan wasan ya ƙi amince wa zama a keɓance daga tawagar Portugal, inda ya tirje akan tafiya tare da ƙasar domin jagorantar ta.

Reuters ta ruwaito cewa, al’amarin ya sauya salo ne a lokacin da Jesus kwatsam ya buƙaci Ronaldo ya buga mintina 30 na ƙarshe na wasan Portugal da Norway. Amma duk da ɗan wasan ya yi ƙwarya-ƙwaryan atisaye, kocin bai yi amfani da shi a wasan ba har aka kammala, wanda ke nuna mai horarwar ya saɓa alƙawarinsa. Wannan al’amari ya sa cikin fushi Ronaldo ya fice daga filin wasan ba tare da miƙa gaisuwa ga magoya baya ba, ɗabi’ar da ta sanya ɗan wasan bayar da haƙuri a yanzu.

Wani rahoto ya nuna cewa, daraktan wasannin Al Nassr, Simao Coutinho ya shiga tsakani wajen sulhunta ɓangarorin biyu. An buƙaci kocin ya bayyana wa ‘yan jarida cewa Ronaldo bai buƙaci buga wasan na Norway ba a karan kansa kuma atisayen da ya yi kure ne na salon wasa.

Ronaldo dai ya yi iƙirarin kocin ya saɓa masa alƙawari a tattaunawar da suka yi a baya, ciki har da cewa yana daga cikin ‘yan wasan yake son tafiya tare da su a shirinsa na jagorantar ƙungiyar. A halin yanzu ana jiran ji ta bakin masu ruwa da tsaki a harkokin ƙwallon ƙafan Portugal musamman kan wannan tsama da ta sanya masu kallo cece-kuce kan makomar zakaran ɗan wasan da ya shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar ƙasar a matakai daban-daban.

By Babaji

Leave a Reply