
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta jaddada tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin ɗan takarar Sanatan Jihar Kogi ta Tsakiya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a zaɓukan 2027 da ke tafe.
A hukuncinsa na ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba, 2026, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya yi watsi da ƙorafin da Momo Obaro ya shigar wa kotun, wanda ya ƙalubalanci ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin jam’iyyar a watan Mayun 2026. Alƙalin ya ce, Obaro ya gaza jure wa biyayya ga hanyoyin warware rikicin cikin gida na APC gabanin tunkarar kotun kan matsalar takarar.
Mai Shari’a Ekwo ya ce, duk da cewa mai ƙarar ya miƙa ƙorafi ga Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na jam’iyyar, ya kasa kai wa Kwamitin Zartarwarta ta Ƙasa (NWC) kamar dokokin jam’iyyar suka hukunta, yana mai kafa hujja da Sakin-Layi na 15(3) na kundin dokokin APC.
Haka kuma, kotun ta ce hujjojin da Obaro ya gabatar ba su samu sanya hannu ba don haka ba su da nagartar da za a yi aiki akansu. Daga nan ne alƙalin ya yi watsi da ƙorafin bisa rashin nagarta da kuma umartar kowane ɓangare ya ɗauki nauyin abin da ya kashe kan shari’ar.
Yahaya Bello, wanda ya jagoranci Jihar Kogi daga 2016 zuwa 2024, na neman sake dawo wa ofishin gwamnati ne ta zaɓen sanatan 2027. Bayyanarsa a matsayin ɗan takarar APC ya nuna cewa zai kara da ‘yar takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar kuma sanata mai ci, wato Natasha Akpoti-Uduaghan a zaɓen da ke ƙaratowa.
