
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU) reshen Jihar Zamfara, ta ce ta tsunduma a yajin aiki mara iyaka sakamakon abin da ta kira da gazawar warware matsalolinta daga ɓangaren Gwamnan Jihar Zamfara.
Buƙatun sun haɗa da neman gwamnatin ta aiwatar da yarjejeniyar albashi da biyan wasu haƙƙoƙin mambobinta da aka yi tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya a baya. Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin wani zaman kwamitin zartarwarta da aka gudanar a ranar Talata a farfajiyar jami’ar na wucin-gadi da ke Talatan Mafara.
Da yake jawabi a taron, Shugaban riƙo na ƙungiyar, Kwamared Anas Abubakar Dogo, ya zargi gwamnatin da gazawa wajen warware matsaloli da dama da ke addabar lakcarori ta hanyoyin da aka amince da su a hukumance.
Ya bayyana cewa, sun ɗauki matakin ne biyo bayan ƙarewar wa’adin da suka bayar da yajin aikin gargaɗi da ƙungiyar ta sanar da fari ba tare da samun wani ci-gaba kyau ba. A cewarsa, ba za ta bada tabbacin cigaba da gudanar da harkokin karatu ba ba tare da biyan buƙatun nasu ba, waɗanda daga ciki akwai yarjejeniyar albashi.
Haka kuma, ASUU ta roƙi ɗalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga cikin al’amarin don maslahar ilimi a Jihar Zamfara da ma Arewa maso yammacin Nijeriya baki ɗaya.
